News
Hukumar Hisbah Ta Kama Kwamishina Bisa Zargin Sa Da Lalata Da Matar Aure A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar Hisbah ta Kano ta kama wani kwamishinan Jigawa bisa zargin sa da lalata da matar aure.
Kwamishinan da hukumar ba ta bayyana sunansa ba, ya shiga hannu ne bayan ƙarar da mijinta ya shigar, inda yake zargin matar kuma uwar ’ya’yansa biyu na lalata da kwamishinan a bayan idonsa.
Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 1.289 A Cikin Watan Satumba
Wani jami’in hukumar ta Hisbah da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana na cewa sun kama kwamishinan da matar ne bayan jami’an Hisbar da mijin matar sun rutsa su a wani kango mallakin kwamishinan a cikin mota.
Ganin su ne kuma ya sanya matar ta yi yunƙurin guduwa a motar, inda ta buge mai gadin, kafin rundunar Hisbah ta samu nasarar tsayar da ita da nasu motocin.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
