News
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hedikwatar Tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 101 sun kama wasu 182 da a ciki akwai kwamandan gungun mahara mai suna Usman Maisaje a cikin mako daya a kasar nan.
Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka a Abuja.
Tawagar ‘Yanwasan Kano Pillars Sun Yi Hatsari A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Filato
Buba ya ce sojojin sun ceto mutum 157 da aka yi garkuwa da su sannan Maisaje makusancin shahararren dan ta’adda Kachalla Bola ne wanda jami’an tsaron suke nema ruwa a jallo.
Ya ce Maisaje na taimaka wa jami’an tsaron wajen basu bayanan sirri don kamo sauran ‘yan ta’adda a kasar nan.
Bindigogi 71, AK-47 50, bindigogi kirar hannu 16, bindigar mafarauta biyar, Pump action biyar da harsasai da dama, rediyo daya, motoci 19, babura 23 da wayoyin hannu 35 na daga cikin ababen da dakarun suka kama.
A Arewa maso Gabashin Najeriya, Buba ya ce sojojin dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan ta’adda 54 sun kama wasu 71 sannan sun ceto mutum 39 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce dakarun sun kama makamai da dama sannan ‘yan ta’adda 74 in da a cikin su akwai maza 7 mata 17 da yara 44 sun mika wuya ga hannun jami’an tsaron.
Buba ya ce rundunar sojin sama ta yi wa ‘yan ta’adda ruwan bamabamai a dakin Bukar Meram dake kusa da Tumbuns inda suka kashe mahara da dama a wurin.
A Arewa ta Tsakiya dakarun dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ‘Whirl Stroke’ sun kashe mahara 12 sun kama wasu 42 sannan sun ceto mutum 56 da aka yi garkuwa da su.
A Arewa maso Yamma rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ da ‘Whirl Punch’ sun kashe mahara 28, sun kama wasu 57, sun ceto mutum 44 da aka yi garkuwa da su tare da kama makamai da dama.
Buba ya ce rundunar sojin sama ta kai wa mabuyar dan bindiga Malam Yaddi hari a dakin Jan Birnin Gwari dake jihar Kaduna.
A Neja-Delta rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun ragargazza matatar mai 60, rijiyoyin mai 4, jiragen ruwa 48, banbu 52 da tankuna 38.
Ya ce jiragen ruwa biyu, murhun girka abinci 55, keke NAPEP daya, wayoyin hannu shida da motoci na daga cikin kayan da dakarun suka kama.
Sojojin sun Kuma kama lita 712,535 na bakin mai, lita 76,8000 na diesel da mutum 45 dake da alaka da satar man fetur.
A Kudu maso Gabas Buba ya ce rundunar ‘Operation UDO KA’ sun kashe mahara 7, sun kama wasu 12 sannan sun ceto mutum 18 da aka yi garkuwa da su.
