News
Tsananin Rashin Wutar Lantarki Da Masifar Rashin Ruwa Ya Jefa Mutane Da Dama Cikin Halin Ha’ula’i A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Faɗuwar babban layi wutar lantarki na jihohin Arewa ya jefa jjhohin cikin matsanancin hali, inda al’umma a Kano suka fara kokawa saboda tsayarwar komai waje guda da kuma fama da duhu da suke yi da daddare ga Matsalar Rashin Ruwa.
A halin yanzu dai da yawan kasuwanci da suka dogara da wutar lantarkin sun tsaya cak a yayin da ake cigaba da fuskantar tsadar man fetur da ruwan sha a jihar.
WANE DAN WASA NE ZAI IYA LASHE KYAUTAR BALLON D’OR TA SHEKARAR 2024?
A baya dai a irin wannan yanayi al’umma kan koma ne su rugumi injinan ganerata, amma tsadar man fetur ya sanya su cikin tsaka mai wuya, gaba kura baya sayaki.
Haka zalika da yawan ‘yan kasuwa kan zauna a shagunansu cikin tsafi da ƙunci wanda ya hakan ke tilasta musu yin ciniki daga wajen shago saboda a sha iska.
Idan kuwa ana maganar ruwan sanyi a yayin da ake tsala matsananciyar rana, to fa abin ba sauƙi domin rashin wutar ya sanya ana fama da ƙarancin ruwan sanyi kuma ko da masu sayar da ruwan ba safai ya cika yi sanyin da zai gamsar ba.
Wanann na zuwa ne a lokacin da al’ummar ke fama da rashin wutar lantarki na tsawon kwanaki ba tare da jin wani yunƙuri daga gwamnatin jihar Kano ba na nemo wa al’umma mafita kamar yadda wasu da suka buƙaci a ɓoye sunansu suka bayyana wakinmu
