News
Wata Tanka Ɗauke Da Silindar Gas Ta Fashe A Wani Gidan Mai A Katsina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD TUKUNTAWA
Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa wani tankar gas dauke da silindar ta fashe a wani Gidan mai da ke karamar hukumar Jibia, wanda ya jawo barna mai yawa tare da lalata motoci guda shida.
Mai magana da yawun hukumar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a a Katsina.
“A ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba, jami’an ‘yan sanda na hedikwatar ‘yan sanda ta yankin Jibia sun ji wani kara mai karfi. Babban Sufeton ‘Yan Sandan yankin (DPO), tare da wata tawaga da hadin gwiwar sojoji, sun gaggauta zuwa wurin da abin ya faru,” in ji Sadiq-Aliyu.
Ya bayyana cewa, bayan isowarsu wurin Gidan mai, sun tarar da wata tanka dauke da silindar gas tana ci da wuta a gidan Tamal da ke kan hanyar Kagadama-Magamar Jibia.
“Tawagar ta hadin gwiwa ta gaggauta daukar matakan kare rayuka da kuma rage asarar dukiya, inda suka yi nasarar kashe wutar.
Motoci guda shida sun lalace sakamakon gobarar, amma babu asarar rai,
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Malam Aliyu Abubakar-Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin fashewar.
Sadiq-Aliyu ya tabbatar da cewa za a ci gaba da bayar da rahotanni yayin da binciken ke tafiya.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
