Connect with us

News

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu da ake zargin‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani babban jami’in hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA tare da hadimin sa a kusa da babban ofishin hukumar da ke kan hanyar Isah-Ogwashi-Uku a karamar hukumar Aniocha ta Kudu a jihar Delta.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a a lokacin da jami’in ke kan hanyar sa ta komawa gida.

Rikicin Masarautar Kano : Kashim Shattima Ya Ayyyana Sunusi Lamido A Matsayain Sarki Na Goma Sha Shida

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun yi kwanton bauna ne a kan hanya inda suka tilasta masa shiga wata mota da babu lamba a jikinta.

Advertisement

Da yake magana kan lamarin, wata majiya ta kusa da hukumar ta ce, “Da alama masu garkuwa sun sanya ido ne akan jami’in. wanda hakan ke nuni da cewa sun dade suna bibiyar sa.”

Bincike ya nuna cewa Wannan garkuwa da aka yi shine karo na biyar cikin kwanaki goma da aka yi garkuwa da mutane a garin Ogwashi-Uka.

Advertisement

A cikin wanda ya faru a baya-bayan nan, an harbe wasu matasa biyu har lahira yayin da wasu biyu kuma aka yi garkuwa da su a hanyar Edo-Otulu da ke Agidiase Quarters.

A yanzu haka dai Mazauna garin Ogwashi-Uku sun bayyana fargaba tsoro game da yadda rashin tsaro ke cigaba da karuwa a yankin.

Advertisement

“Bamu da kwanciyar hankali a yankin mu, Dole ne gwamnati ta yi gaggawar magance wannan matsalar kafin a samu asarar rayuka da yawa,” wani shugaban yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana.

Sai dai kuma Majiyoyin tsaro sun yi nuni da cewa masu garkuwan da alama sun suna da wani makusancin wanda aka sace da ke basu bayani,duba da yanzu sun chanza salon garkuwa.

Advertisement

“Da alama dai masu garkuwan suna da wanda ke kawo musu rahoto akan hukumomi” cewar wata majiya.

Da aka tuntubi kakakin hukumar NDLEA reshen jihar Delta, Mista John Kennedy bai ce komai ba game da lamarin.

Advertisement

Rahotanni sin bayyana cewa a yanzu haka ana ci gaba da kokarin gano jami’in da aka sace tare da hadimin sa .

 

Advertisement

 

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending