News
Majalisar Matasan Arewa Ta Yi Allah-Wadai Da Sanata Barau Jibrin Da Ya Tallafawa Kudirin Gyaran Harajin Da Zai Kassara Tattalin Arzikin Arewa.
Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin,
Majalisar Matasan Arewa, a madadin shugabannin matasa na jihohi 19 na Arewacin Najeriya, tana bayyana matukar bacin ranta da takaici dangane da halayenka na karkatar da tsarin don tabbatar da karantun kudirin gyaran haraji, karo na biyu na wanda ya kunshi wata mummunar manufa wacce za ta kassara tattalin arzikin Arewa.
Wannan abin kunya naka na goyon bayan kudirin Shugaba Tinubu da ya shafi gyaran haraji, ya nuna tsananin rashin damuwarka ga matsalolin tattalin arziki da kasuwanci na mazabarka, Jihar Kano, da gaba daya Arewacin Najeriya.
A matsayinmu na wakilan matasan Arewa, muna da tabbacin cewa wannan kudirin gyaran haraji, a wannan tsarin da ake gabatarwa, zai yi mummunar illa ga tattalin arziki da burin mutanenmu.
Wannan ya kara tabbatar da rashin la’akari da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.
Abin takaicin shine yadda ka yi amfani da karfin ikonka a Majalisa don tilasta ra’ayinka da burin kanka na siyasa, don faranta wa ‘yan bangarorin da suka yi maka alkawarin sama da kasa zuwa shekarar 2027.
Duk da matsalolin da Arewa ke fuskanta kamar karancin wutar lantarki, rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, da gazawar ababen more rayuwa, ka zabi ka fifita kudiri mai illar gaske ga mutanen Arewa.
Muna tunatar da kai cewa an zabe ka ne domin ka yi aiki don ciyar da Arewa gaba ta hanyar amfani da ikonka na majalisa, ba domin ka tsaya tsayin daka wajen tallafa wa manufofi masu illar Arewa ba.
Muna sanar da kai cewa Majalisar Matasan Arewa tana matukar bacin rai da kai da duk masu irin ra’ayinka da ke shirin yin kutse wajen lalata makomar Arewa.
Za mu yi amfani da karfinmu don bayyana gaskiya game da kai da , wadanda suka kuduri aniyar sayar da makomar Arewacin Najeriya don ribar siyasa.
Wannan kudirin gyaran haraji da gwamnatin Shugaba Tinubu ke gabatarwa ya sha kin amincewa daga Kwamitin Shawara kan Tattalin Arzikin Kasa da Gwamnonin Arewa, amma kai ka dage wajen goyon bayansa domin burin siyasa mara tushe.
Muna shawartar ka da ka gyara halinka kafin mutanen Arewa gaba daya—tsaffi da yara, mata da maza—su tashi su yi addu’a a kanka.
sanya hannu:
1. Usman Alhaji Musa – Jihar Yobe
2. Sulaiman Idris Yusuf – Jihar Kano
3. Aminu Shehu – Jihar Jigawa
4. Nura Abba Ali – Jihar Katsina
5. Abdurrashid Sa’ad – Jihar Zamfara
6. Muhammadu Bello – Jihar Kebbi
7. Yakubu Abubakar – Jihar Sakkwato
8. Dr. Mu’azu Tadama (PhD) – Jihar Kaduna
9. Isma’il Alhassan Musa – Jihar Bauchi
10. Maryam Adam – Jihar Gombe
11. Muktar Abdul – Jihar Taraba
12. Abdulhamid Musa – Jihar Adamawa
13. Alh. Mai Tijjani – Jihar Borno
14. Sabi’u Musa – Jihar Filato
15. Aliyu Dogara – Jihar Nasarawa
16. Grace O. Ojochogwu – Jihar Kogi
17. Mohammed Kuta Muhammad – Jihar Kwara
18. Shehu Idris – Jihar Neja
19. Engr. Zakaria M. Zakaria – FCT
20. Oko Sunday – Jihar Benue
21. Comrade Adikwu Omaji Joshua –
Sakataren Yada Labarai na Kasa
Dr. Abdulhafiz Garba, PhD, Sakataren Majalisa
r Matasan Arewa na Kasa
Ali Mohammed Idris, PhD, Shugaban Majalisar Matasan Arewa
