News
Shugaba Tinubu Da Manyan Yan Siyasa Sun Halarci Daurin Auren Ya’yan Sanata Barau Jibril Maliya
- DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yau Juma’a aka gudanar da daura Auren Ya’yan mataimakin shugaban majalisssar dattatwan Sanata Barau Jibril Maliya Yar gidan Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da Dan Gidan Abdulmunaf Sarina.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas da Gwamnoni da dama da Sanatoci ne suka Halarci taran daurin Auren.
Haka zalika Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da dan gidan tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari Yusuf Buhari da Mamman Daura suma suna daga cikin manyan baki a wajen daurin Auren.
Jaridar Inda ranka ta rawaito cewa dan Sanata Barau, Jibrin Abba Barau shine ya auri Maryam Nasir Ado Bayero, Yar Sarkin Bichi sai kuma Aisha Barau Jibrin wanda aka daura auren ta da Injiniya Abubakar, Da’.ga Dr Abdulmunaf Yunusa Sarina, shugaban rukunin kamfanonin Azman.
Rahotanni sun tabbar da cewa shugaba Tinubu ne ya zamto a matsayin Wakili da Waliyyi ga ‘ya’yan mataimakin shugaban majalisar dattawa ta bakin kakakin majalisar wakilai tajuddin Abbas.
A yayin da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Dr Abdullahi Ganduje ya kasance Waliyyi ga diyar Sarkin Bichi, a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura, ya kasance Wakili na Abubakar, dan Dakta Abdulmunaf Sarina Wanda Limamin masallaci na kasa Farfesa Ibrahim Maqari ya jagoranta.
Cikin manyan bakin da suka halarci daurin Auren sun hadar da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq da Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah; Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda.
Sai kuma hwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da dai sauransu manyan baki daga gida da wajen Nageriya.
Cikin Sanatocin da suka halarci taron Auren sune shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da Ali Ndume da Sani Musa, Ibrahim Mohammed Boma da Aminu Iya Abbas da Buhari Abdulfatai da Mohammed Tahir Monguno da Ikira Aliyu Bilbis da Mohammed Ogoshi Onawo da Salihu Mustapha da Shehu Buba da Abdul Ningi da Abdullahi Yahaya da Ahmed Lawan da Sahabi Ya’u da Kamorudeen Adekunle Adedibu, Danjuma Goje.da Lawal Usman da Kawu Sumaila.
Wakilan majalisar ECOWAS duk sun halarci taron da mataimakin shugaban majalisar na hudu, Billay G Tunkara.
Mataimakan shugaban kasa da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, shugaban ma’aikata, tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt Hon Femi Gbajabiamila, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, mataimaki na musamman kan harkokin tsaro. Shugaban (Al’amuran Siyasa), Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa Kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz, duk sun halarci taron
