Connect with us

News

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni sun ce jirgin ya kai harin ne kan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa da ke yankin karamar hukumar Silame a jihar ta Sokoto.

Advertisement

Bayanai sun ce jirgin yayi kuskure ne wajen kai harin inda ya zaci ko mutanen kauyukan biyu mayakan ‘yan ta’addar LAKURAWA ne.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un :Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Gwamnan Jigawa Rasuwa

Wannan lamari dai ya zama ruwan dare a Najeriya , a lokuta da dama a baya Jiragen yakin rundunar sojin saman Najeriya ya sha jefa boma-bomai akan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending