Connect with us

News

RASHIN BIYAN ALBASHI: An Kama Jagororin Zanga-zangar Malaman Makaranta 

Published

on

An kama jagororin zanga zangar rashin biyan albashi da malaman makaranta keyi a

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Fiye da malaman makaranta 3,000 daga kananan hukumomi 13 na Jihar Ebonyi suka  gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi a Abakaliki, babban birnin jihar, bisa rashin biyan albashin watanni uku da shugabannin kananan hukumomin jihar suka ki biya.

Advertisement

Haka zalika Malaman Makarantar da suka gudanar da zanga zanag sun nuna rashin amincewa da shugabannin kananan hukumomi 13, sabida zargin rashin biyan albashin ya haifar da mutuwar malaman makaranta uku a ranar Kirsimeti.

Na Godewa Abba Da Ya Gwale Masu Neman Ya Tsaya Da Ƙafar Sa  —Kwankwaso

A baya-bayan nan, Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bai wa shugabannin kananan hukumomin wa’adin sa’o’i 24 domin biyan malaman albashinsu don su samu damar yin bikin Kirsimeti kamar sauran ma’aikata a jihar.

Advertisement

Sai dai, a yayin da kwamishinan ilimi na jihar, Mista Paul Awo Nwabosi, ya gana da shugabannin masu zanga-zanga, ya yi barazanar daukar mataki a kansu maimakon sauraron korafinsu.

Kwamishinan ya bayar da umarnin kama shugabannin zanga-zangar, inda aka tilasta musu shiga wata motar Hilux da aka ajiye a wurin.

Advertisement

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending