News
Hana ‘Yan Majalisa Saka Wani Abu Cikin Kasafin Kudi Shi Ne Kawai Zai mAgance Matsar Cushe —Shehu Sani
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohondan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya tsara daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen dakatar da cushe a cikin kasafin kudi a Najeriya.
A wani sako da ya fitar a shafin sa X a ranar Talata, tsohon Sanatan ya ce hanya daya tilo da za a dakatar da tafka cushe a kasafin kudi shi ne a kafa dokar da ta haramtawa ‘yan majalisa yin katsalandan akasafin kudin da ma’aikatu da hukumomi, na gwamnatin tarayya suka gabatar.
Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Bijiro Da Sauye-sauyen “Da Suka Zama Dole” Domin Gina Ƙasa —Shugaba Tinubu
Sai dai ya ce yana shakkar ko ‘yan majalisar za su so a kafa dokar da za ta dakatar da irin wannan aika-aika, ko kuma za a bar irin wannan kudirin ya daidaita.
Shawarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron kwamitin kasafin kudi tare da Ministan Kudi da Ministan Tattalin Arziki, Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki da Darakta Janar, Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, a ranar Talata, 7 ga Janairu, 2025. .
Hakanan za a gudanar da kare kasafin kuɗi na ƙananan kwamitoci tare Hukumomin Gwamnatin masu dacewa daga Laraba 8 ga Laraba 15 ga Janairu 2025.
