News
Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Yar Sakataren Gwamnatin Sokoto Da Jikokin Sa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa, ya rasa ‘yar sa da kuma ‘ya’yan ta guda uku sakamakon wata gobara da ta cinye dukkan gidan su a safiyar Litinin.
Wanda suka rasu sun haɗa da matar Alhaji Muhammadu Yusuf Bello, sakataren dindindin na ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa ta Jihar Sokoto.
Yan Sanda Sun Kama Mutum 50 Da Zargin Sace Murafen Kwatami A Kan Tituna
Rahotanni na nuni da cewa wutar ta lalata gidan gaba ɗaya yayin da iyalin suke barci, inda shi kaɗai mijin matar ya tsira.
A lokacin da wakilin Blueprint ya ziyarci wurin, ba a samu tabbacin ainihin sanadin wutar ba, sai dai bincike na ci gaba don gano musabbabin wannan mummunan al’amari.
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Sokoto sun ɗauki awanni da dama suna yaƙi da wutar kafin su samu nasarar kashe ta.
An gudanar da jana’izar waɗanda suka rasu a masallacin Juma’a na garin Sifawa, cikin ƙaramar hukumar Bodinga, inda aka binne su bisa ƙa’idojin addinin Musulunci.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
