News
Alh. Usman Sa’idu Santurakin Kupto ya Dauki Nauyin Tallafawa Matasa Da Mata
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A matsayin wani bangare na kokarinsa na taimakawa al’umma, Alhaji Usman Sa’idu, wanda aka fi sani da Santurakin Kupto, ya dauki nauyin koyawa matasa sana’o’i daban-daban domin inganta rayuwarsu.
Wannan tsari ya shafi matasa maza da mata daga sassa daban-daban na yankin.
Baya ga haka, Santurakin Kupto ya bayar da tallafin naira dubu goma-goma (₦10,000) ga mata a kowanne ward, domin tallafa musu wajen bunkasa sana’o’insu da habaka tattalin arzikin iyalansu.
A wani karin kokari don samar da aikin yi, Santurakin Kupto ya samar da damar samun aikin soja ga matasa, wanda zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin su, tare da samar da mafita mai dorewa ga ci gaban rayuwar matasa.
Wannan kyakkyawan aiki ya sake tabbatar da jajircewar Alh. Usman Sa’idu Santurakin Kupto wajen kula da ci gaban al’umma da tallafawa dukkan sassa na jama’a.
