News
Jaridar Inda ranka Na Gayyatar Yan Uwa Da Abokan Arziƙi Zuwa Wajen Daurin Auren Abul Abbas Adamu Sidi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A Madadin hukumar gudanarwa ta Jaridar Inda ranka da kungiyar Tijjanawan Kwankwasiyya Farum ke gayyatar yan Uwa da Abokan arziƙi zuwa wajen daurin Auren Abul Abbas Adamu Sidi da akafi sani da (Abul Abbas)
Abul dai ya kasanc e daya ne daga cikin Shuwagabannin Kungiyar Tijjanawan Kwankwasiyya Farum reshen Jihar Kano dake ruke da mukamin Maga Takarda wato Secretary dake bata gudunmawa ta fuskoki daban daban da’ma taimakon wasu kungiyoyin dake fafutuka akan rayuwar Jama’a domin ganin rayuwarsu ta Inganta.
Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kano Na Neman Alhajiji Nagoda Ruwa A Jallo
Haka zalika Abul dan gwagarmanaya ne kuma Mutun ne na Muta ne dake girmama kowacce irin halitta musamman ma Mutun Dan Adam Da Allah Ubangiji ya karrama.
Ya kasance wata Katanga a wajen Al’umma da dama ciki kuwa harda Jaridar Inda ranka.
A gefe guda kuma Abdul ya kasance dan Kasuwa ne da’ke kasuwancinsa a kasuwar sai’da tufafi ta ( Kwari ) a gidan Gareji Shagon Shari Mai Fisis mai lamba 1 Mai dake saman Bene.
Za’ayi wannnan daurin Auren ne a ranar Lahadi 19 January 2025 a Gwammaja Masallacin Isa Kafinta dake Jihar Kano da misalin karfe 11:30 na Safe.
Idan Kuma ba’a sami damar halartaba ayiwa Ango Da Amarya Addu’a da fatan alkhairi.
Da fatan Allah Ubangiji ya bada ikon halarta amin summm amin.
