Connect with us

Uncategorized

Wani Mutum Mai Shekaru 45 Ya Mutu A Cikin Rijiya A Kano

Published

on

IMG 20250122 WA0009

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ciro gawar wani mutum da ba a san ko waye ba mai kimanin shekaru 45 daga wata rijiya a kauyen Babawa da ke karamar hukumar Gezawa, Jihar Kano.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, mai magana da yawun hukumar, Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa ofishin hukumar ya samu kiran neman agaji dangane da lamarin ranar Talata.

LABARI DA DUMI-DUMI: An saki matar Ekweremadu daga gidan yari A  Burtaniya

Masu aikin gaggawa sun hanzarta isa wurin inda suka ciro gawar daga rijiyar.

Sai dai har yanzu ba a san yadda mutumin ya fada rijiyar ba. Hukumomi na ci gaba da bincike don gano musabbabin lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending