News
Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kama Jami’an Karamar Hukumar Nasarawa da Hadimin Gwamna Bisa Zargin Karkatar da Naira Miliyan 105
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaki da rashawa ta jihar kano karkashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta cafke wasu jami’an Karamar Hukumar Nasarawa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna, Mustapha Maifada, bisa zargin karkatar da Naira miliyan 105.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa jami’an da aka kama sun hada da Daraktan Kula da Ma’aikata da Ma’ajin Kudi na Karamar Hukumar Nasarawa.
A Yi Siyasa Cikin Mutunci Da Girmamawa – Waiya Ga ‘Yan Adawa
Rahotanni sun nuna cewa an umarce su da su baiwa Mustapha Maifada Naira dubu dari da biyar domin gudanar da wani shiri.
Sai dai, maimakon haka, sun aika masa da Naira miliyan dari da biyar, lamarin da suka bayyana a matsayin “kuskure.”
Bincike ya nuna cewa Mustapha Maifada ya fara amfani da kudin da aka aika masa, inda ake zargin ya sayi kadarori da mota. Wannan lamari ya faru ne tun a watan Nuwamba na shekarar 2024.
A halin yanzu, hukumar Anti-Corruption karkashin Barista Muhuyi na ci gaba da tsare wadanda ake zargi domin fadada bincike kan lamarin.
