News
Gwamnatin Kano Ta Kuduri Aniyar Kawar Da Mace-macen Mata Masu Juna Biyu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa manufarta ita ce kawar da mace-macen mata masu juna biyu gaba ɗaya, ba ragewa kacal ba.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dokta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana haka yayin da yake jawabi a taron Dandalin Haɗin Kan Abokan Haɗin Kai (PCF) da aka gudanar a birnin Kano.
PCF wata sabuwar manufa ce da Kwamishinan ya ƙirƙira domin haɗa duk masu ruwa da tsaki a fannin lafiya, tare da tabbatar da cewa ana aiki bisa tsari guda ba tare da maimaita ayyuka ba.
Ya ce gwamnatin Jihar Kano ta himmatu wajen sauya fannin lafiya, bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda a cikin shekara ɗaya da rabi ya gyara manyan cibiyoyin lafiya da kuma ba da kwangilolin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 200.
Dokta Labaran ya jaddada cewa wannan shiri yana daidai da manufar gwamnati na tabbatar da ingantaccen hidima a cibiyoyin lafiya na matakin farko da na biyu, tare da ba da fifiko ga lafiyar mata da yara, musamman kokarin kawar da mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.
Ya bayyana damuwarsa kan kididdigar da ke nuna cewa sama da kashi 70% na mata a Jihar Kano ba sa zuwa asibiti lokacin haihuwa, inda suka fi son haihuwa a gida saboda rashin amincewa da ingancin kulawa a asibitoci.
“A kan haka ne muke gyara asibitocinmu da inganta cibiyoyinmu na matakin farko .
Kwamishinan ya jaddada cewa wannan wani bangare ne na shirye-shiryen gwamnatin Jihar Kano na kawar da mace-macen mata gaba ɗaya.
