Connect with us

News

Ba Sauya Jam’iyya Ke Da Muhimmanci Ba, Sai Sauya Gurbataccen Tunani Don Ceto Arewacin Najeriya 

Published

on

download (1)

 

Shugaban Kungiyar Who Is Fixing The North?, Mustapha Dawood (Sir Sa’e), ya bukaci ‘yan Arewacin Najeriya da su daina mayar da hankali kacokan kan jam’iyyun siyasa, a maimakon haka su mayar da hankali kan sauya tunani da fahimtar yadda ake zabar shugabanni nagari.

Advertisement

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, Sir Sa’e ya bayyana cewa:

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne sauya tsarin da ke jefa kasa cikin wahala, ba wai kawai sauya jam’iyya ba. Dole ne mu dasa tunani mai kyau a zukatan ‘yan Najeriya, domin su fahimci yadda ake zabar shugabanni nagari masu kishin kasa.”

Advertisement

Yadda Matar Aure Ta Rasu A Cikin Masallaci Yayin Tafsirin Ramadan

Ya ce muddin aka kawar da jahilci da son kai a zukatan ‘yan kasa, Najeriya za ta iya kafa gwamnati mai inganci da kowa zai yi alfahari da ita.

Ya kuma bukaci matasa da su kara karfafa tunaninsu ta hanyar halartar taruka masu ilmantarwa a sassan jihohi. A cewarsa, shirya irin wadannan taruka zai taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ga matasa da kasa baki daya.

Advertisement

Sir Sa’e ya jaddada cewa lokaci ya yi da ‘yan kasa za su fahimci cewa ci gaban Najeriya yana hannunsu, ba hannun jam’iyyun siyasa kadai ba. Don haka, ya bukaci a mayar da hankali kan gyaran tunani da ilmantar da mutane kan yadda za su zabi shugabanni nagari da za su fitar da kasa daga halin da take ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending