News
Dan Bijilanti Ya Harbe Kansa Yayin Da Yake Kokarin Cafke Wani A Abuja
Wani dan Bijilanti mai suna Mujahid Ibrahim, mai shekaru 32, ya harbe kansa a kafafu yayin da yake kokarin tsoratar da wani mutumi a unguwar Dei-Dei, Bwari, Abuja.
Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito cewa lamarin ya faru da misalin karfe 12 na dare a ranar Laraba, lokacin da Ibrahim da abokin aikinsa suka tare wani mazaunin unguwar da suke gadin. A cewarsa, mutumin ya karya dokar yankin ta hana zirga-zirga bayan karfe 11 na dare.
A yayin kokarin tsoratar da mutumin, Ibrahim ya harba bindigarsa sama, amma daga bisani, a yayin da yake gudu, bindigar ta sake harba harsasai da suka same shi a kafafu.
Akalla harsasai bakwai aka fitar daga jikinsa, kuma yana jiran sakamakon hoto don gano ko har yanzu akwai sauran a jikinsa.
Abokin aikinsa, Ben Isaac, ya bayyana cewa mutumin da aka tare ya tsere, amma babban yayansa ya dauki nauyin jinyar Ibrahim. An ba shi wa’adin sa’o’i 24 don bayyana kansa ko a kama shi.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
