News
Kungiyar SERAP Ta Bukaci Gwamnati Ta Fara Bincike Kan Bacewar Biliyan 233 Kafin Karɓar Sabon Bashi
Kungiyar SERAP ta bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da shirin karɓar sabon bashin dala biliyan $1.08 daga Bankin Duniya, har sai an gudanar da cikakken bincike kan bacewar Naira biliyan 233 daga hannun Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Najeriya (NBET), da wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs).
A wata sanarwa da ta fitar, SERAP ta jaddada cewa kamata ya yi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen gano inda kudaden suka shiga, maimakon ci gaba da karɓar bashi da zai kara nauyi kan ‘yan kasa. Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya umurci Babban Lauyan Ƙasa, Mista Lateef Fagbemi (SAN), tare da hukumar EFCC da ICPC da su gaggauta gudanar da bincike, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu, da kuma dawo da kudaden zuwa baitul mali.
Yadda Gwamnoni 20 Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashin Dubu 70,000
SERAP ta bayyana cewa matakin karɓar bashi ba zai amfani ‘yan Najeriya matuka ba, musamman ganin yadda gwamnati ke kasa magance batun bacewar makudan kudade. Ta kuma ce cika gibi a kasafin kuɗi na shekarar 2025 da rage nauyin bashi zai fi amfani idan an dawo da wadancan kudaden.
A cewar kungiyar, wannan bukata ta yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na yaki da cin hanci da rashawa.
Bankin Duniya ya bayyana cewa sabon bashin zai taimaka wajen inganta harkar ilimi, ƙarfafa iyalai da kuma abinci mai gina jiki ga marasa galihu. Sai dai SERAP na ganin akwai hanyoyin cikin gida da za a iya amfani da su, idan aka yi gaskiya da rikon amana.
-
Opinion3 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
