News
ADG Care Foundation Ta Kaddamar Da Tallafi A Makarantun Sakandare 13 A Kano
Gidauniyar ADG Care Foundation ƙarƙashin jagorancin Engr. Rabiu Aliyu Garo ta kaddamar da wani muhimmin zagaye na ziyartar makarantun sakandare a ƙananan hukumomi 13 da ke yankin Kano ta Arewa domin tallafa wa ɗalibai da kayan karatu, horaswa, da kuma kyaututtuka masu ƙayatarwa.
An fara wannan zagaye da ƙananan hukumomin Rimin Gado da Kabo, inda aka gudanar da taruka na musamman domin wayar da kan ɗalibai game da yadda za su zaɓi matakin karatun gaba da sakandare cikin hikima da shiri mai kyau. Gidauniyar ta kuma biya wa wasu ɗalibai kuɗin jarrabawar WAEC domin tallafa musu wajen samun damar ci gaba da karatu ba tare da tangarda ba.
Shugaba Tinubu Ya Janye Jerin Sunayen Wadanda Ya Nada Bayan Lura da Kurakurai
Baya ga haka, an raba kayayyakin karatu da kuma kyaututtuka na musamman ga ɗalibai da suka nuna ƙwazo da hazaka a makarantu, alamar ƙarfafa gwiwa da ƙarfafa matasa wajen dagewa da neman ilimi.
Engr. Rabiu Aliyu Garo ya jaddada kudurin gidauniyar wajen ganin kowanne ɗalibi a yankin ya samu ilimi mai nagarta tare da tallafi da shawarwari da za su taimaka masa wajen gina kyakkyawar makoma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
