Connect with us

News

Masu Kwacen Waya Sun Kai Hari Kan Malamar Jinya A Kano

Published

on

satar waya

Wata malamar jinya, Samira Nasiru Zubairu, ta gamu da farmakin wasu da ake zargin ‘yan kwacen waya ne dauke da makami a kusa da Fadar Sarkin Kano a yayin shagulgulan da aka gudanar ranar Lahadi.

Samira, ma’aikaciyar Asibitin Marmara Maternity and Child Hospital da ke Kano, ta shaida wa KANO TIMES cewa lamarin ya faru ne cikin gaggawa a lokacin da take kokarin tsallaka cunkoson da bukukuwan suka haddasa.

Madarasatul Tarbiyatul Aulad Academy Za Ta Yi Bikin Saukar Dalibai 23 A Karo Na Biyu

> “Ina kokarin ketare cunkoso sai wasu samari suka dirar min. Daya daga cikinsu ya sare min hannu da wuka yayin da yake kokarin kwace min waya,” inji ta.

Ta bayyana cewa matasan sun yi amfani da cunkoson motocin wajen aikata ta’asar, inda suka rika kai wa mutane hari babu tsoron jami’an tsaro.

Samira ta ce ta yi ihun neman agaji tana karanta kalmar shahada kafin jami’an hukumar NSCDC su iso su kawo mata dauki. Ko da yake bata rasa wayarta ba, ta samu mummunan rauni a hannunta na dama sakamakon sarewar jijiyarta, wanda ya kai ga garzaya da ita Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin yi mata tiyata.

> “Ina godiya da cewa na tsira da rai, amma abin takaici ne a ce a gaban Fadar Sarkin Kano ake iya kai wa mutum hari,”

Advertisement

A baya-bayan nan dai, hare-haren masu kwacen waya da farmakin matafiya sun zama ruwan dare a wasu sassan Kano, musamman da dare, inda matasa ke amfani da makami wajen aikata fashi.

Sai dai duk da matakan da hukumomin tsaro ke dauka, matsalar ta ci gaba da kamari, abin da ke kara jefa jama’a cikin fargaba.

Samira ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su kara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

> “Ya kamata a tabbatar da cewa kowa na iya yawo cikin gari ba tare da jin tsoron fashi ba,” inji ta.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending