Connect with us

News

Duk Wanda Ke Tunanin Wulakanta Kwankwaso Shi Ne Zai Wulakanta — Gwamnan Kano

Published

on

images (8)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce duk wanda ke ganin zai wulakanta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ne zai ƙare da kunyata kansa.

Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman da tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Baffa Bichi, ya yi, inda ya zargi gwamnatin Kano da ware Naira biliyan biyu duk wata ana tura wa Kwankwaso.

Advertisement

Barazanar Ficewar Meta Ba Za Ta Hana Hukuncin Da Aka Zartar Ba —FCCPC

A cewar Bichi, an kore shi ne daga muƙaminsa saboda ya ƙi amincewa da sahalewa a cigaba da tura kuɗin zuwa asusun jagoran Kwankwasiyya.

Sai dai a jawabinsa yayin wani taro da gwamnan ya yi da kansiloli 484 daga sassa daban-daban na jihar a ranar Lahadi, Gwamna Abba ya ce kalaman Bichi “ba su da amfani, babu hankali, kuma babu tunani a cikinsu.”

Advertisement

Ya ce: “Gwamnati da ba ta cika shekaru biyu ba, ana zargin ta da cin dukiyar jihar fiye da wadda ta gabace ta? Wannan magana ce ta rashin tunani.”

Gwamna Abba ya ce gwamnati ta bai wa Bichi matsayi mai girma, amma sai ya fita yana magana marar tushe da kazafi da sunan ya faɗi gaskiya. Ya ce ya kamata Bichi ya duba kansa ya san me ya sa aka cire shi daga muƙamin.

Advertisement

Gwamnan ya kuma gargaɗe shi da ya daina kai hari ga Kwankwaso, yana mai bayyana shi a matsayin jagora nagari da ya tafiyar da mulki cikin gaskiya da adalci.

Ya ƙara da cewa: “Kwankwaso shugaba ne, kuma nauyin kare mutuncinsa da martabarsa na kanmu ne. Ya kamata kowa ya daina taba muhibbar jagororin da suka sadaukar da rayuwarsu don ci gaban jihar.”

Advertisement

Gwamna Abba ya gargaɗi gidajen rediyo da su daina yada kalaman da za su tayar da zaune tsaye a cikin al’umma, yana mai cewa gwamnati ba za ta yarda da irin wannan dabi’a ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending