News
Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Biliyan 3 Don Biyan Kuɗin Jarabawar NECO, NABTEB Da NBAIS
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe fiye da naira biliyan uku domin biyan kuɗin jarabawen NECO, NABTEB da NBAIS ga ɗaliban da suka cancanta a fadin jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Juma’a.
Ya ce dalibai 141,715 ne suka zauna jarabawar cancantar samun damar rubuta NECO, wato Qualifying Examination, inda kaso 75 cikin 100 daga cikinsu suka samu nasara.
“Wadanda suka ci jarabawar – wato wadanda suka samu credit biyar – su ne gwamnati za ta biya musu kuɗin jarabawen shiga makarantun gaba da sakandire,” inji Kwamishinan.
Makoda ya bayyana cewa, baya ga NECO, ɗaliban da za su rubuta jarabawen National Business and Technical Examinations Board (NABTEB) da kuma National Board for Arabic and Islamic Studies (NBAIS) za su amfana daga tallafin da gwamnati ta ware.
Ya ce, “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya dauka na tallafawa fannin ilimi, kuma yana taya ɗaliban jihar Kano murnar wannan gagarumar nasara.”
Kwamishinan ya kara da cewa, wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnatin Kano na tabbatar da cewa kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi ba tare da tangarda ba.
