News
’Yar Shekara 19 Ta Kashe Kanta Bayan Samun Maki 190 A JAMB
Wata budurwa mai shekara 19, Opesusi Faith Timilehin, ta kashe kanta bayan da ta gaza samun makin da ake buƙata domin samun gurbin karatu a jami’a.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a Odogunyan da ke Ikorodu, Jihar Legas, inda Timilehin ke zaune tare da yayarta.
Turji Ya Tilasta Wa Mutane Fiye Da 5,000 Yin Hijira A Sokoto
Timilehin ta sha gubar beran da gangan, bayan da ta ga sakamakon jarrabawar JAMB inda ta samu maki 190 – maki da bai kai wanda ake buƙata ba domin fannin Microbiology da take so ta karanta.
Wata abokiyar zamanta ta ce wannan shi ne karo na biyu da Timilehin ke rubuta jarrabawar JAMB, kuma ta ce: “Ta ce sakamakon da ta samu bara ya fi na bana kyau.”
Wani daga cikin ’yan uwanta ya bayyana cewa tun da jimawa Timilehin ke fatan shiga jami’a, kuma burinta ne ta samu gurbin karatu a fannin kimiyya.
Bayan ta sha gubar, Timilehin ta je wajen yayarta tana neman man shafawa saboda ciwon ciki. Sai dai yayarta ba ta gane matsalar da wuri ba, sai bayan ta fara ihu tana neman taimako, lamarin da ya sa maƙwabta suka ruga wajen.
An ce an yi kokarin ceton rayuwarta, amma daga bisani ta rasu.
Maƙwabta da suka san Timilehin sun bayyana ta a matsayin yarinya mai hankali da ladabi, kuma sun ce sun girgiza da jin labarin rasuwarta.
Wannan lamari ya sake tayar da ƙayamar da ake yi kan yadda matasa ke ɗaukar matakin kashe kansu sakamakon matsin lamba daga jarrabawa da rayuwa gaba ɗaya.
DAILY NIGERIAN
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
