News
Kashi 2.5% Kacal Na ‘Yan Najeriya Ke Kula Da Matsalar Hawan Jini – NHS
Kungiyar Kula da Masu Hawan Jini ta Najeriya (NHS) ta bayyana cewa kasa da kashi 2.5 cikin 100 na ‘yan Najeriya ne ke kula da lafiyar su dangane da matsalar hawan jini, duk da hadarin da cutar ke haifarwa ga rayuwar dan Adam.
Shugaban kungiyar, Farfesa Simeon Isezuo, ne ya bayyana hakan a wajen bikin Ranar Hawan Jini ta Duniya (WHD), da aka gudanar a ranar Talata a birnin Abuja, karkashin taken: “Yin Gwaji, Kiyayewa, Don Rayuwa Mai Inganci.”
Ya ce binciken da kungiyar ta gudanar ya nuna cewa daya cikin kowane mutane uku da ke zaune a birane na dauke da cutar, yayin da daya cikin kowane hudu a karkara ke fama da ita. Sai dai abin damuwa, a cewarsa, kashi daya cikin kaso uku na masu cutar ne kawai ke da masaniyar cewa suna dauke da ita, kuma kashi 10 cikin 100 daga cikinsu ne ke shan magani yadda ya kamata.
Farfesa Isezuo ya kara da cewa: “A zahiri, kasa da kashi 2.5% ne kacal ke daukar kwararan matakai na kiyayewa da magance cutar. Wannan wani babban gibi ne da ke bukatar daukar matakan gaggawa.”
A cewarsa, rashin sanin mutum na dauke da cutar da wuri na janyo illoli masu tsanani kamar shanyewar jiki, ciwon zuciya, cutar koda da sauran su. Hakan, a cewarsa, na faruwa ne sakamakon rashin yin gwaji akai-akai da kuma sakaci da shan magunguna.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika yin gwajin hawan jini lokaci-lokaci – ko a gida ko a asibiti – da kuma rungumar sauyin rayuwa ta hanyar motsa jiki, rage yawan amfani da gishiri da kayan zaki, da yawaita cin ganye da kayan lambu.
Isezuo ya kuma bukaci gwamnati da ta dauki matakan da suka hada da kara haraji kan kayayyakin da ke haddasa cutar kamar barasa, taba sigari da abincin gwangwani – musamman masu zaki da gishiri – domin dakile yaduwar cutar a cikin al’umma.
Ranar 17 ga watan Mayu ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Hawan Jini ta Duniya, domin wayar da kai kan mahimmancin rigakafin cutar da kuma kiyaye lafiyar zuciya.
