News
YANZU-YANZU: Putin ya kori ma’aikata 1,000 masu bashi tsaro, saboda fargabar kamuwa da guba
Daga mujahid danllami garba
Vladimir Putin ya riga ya san cewa ayyukan da zai yi a nan gaba za su kawo tashin hankali ko da a tsakanin ‘yan kasarsa wani rahoto ya bayyana.
Rahoton ya ce ba zato ba tsammani shugaban na Rasha ya fara korar ma’aikatansa kusan mutane 1,000 ne suka rasa ayyukansu kawo yanzu.
Idan muka ce ma’aikata, muna nufin ma’aikatan Rasha waɗanda a zahiri suke ba shi abincinsa kuma suna kula da shi akai-akai, in ji Marca.
An kuma bayyana cewa, Vladimir Putin yana rike da wani ma’aikaci na musamman wanda ko da yaushe yakan dandana abincinsa kafin ya fara cin abinci.
Duk wannan dabi’a ta zama ruwan dare daga ‘yan kama-karya ko azzalumai wadanda galibi ke tsoron rayukansu.
A bayyane yake cewa tuni Putin ya na yunkurin kisa da yawa daga mutanensa..
-
News1 day ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News3 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
