News
Sarkin Jinkan Hausawan Afrika Ya Jajanta Wa Wadanda Ambaliya Ta Shafa A Jihar Neja

Sarkin Jinkan Hausawan Afrika, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim (Abba Alra-iwas), ya bayyana matukar alhini da jimamin sa kan iftila’in ambaliyar ruwa da ya afku a wasu sassan Jihar Neja, wanda ya janyo asarar dukiyoyi da raba jama’a da muhallansu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ambasada Abba Alra-iwas ya ce wannan iftila’i babban jarrabawa ne ga al’umma, kuma lokaci ne na nuna tausayi da goyon baya ga juna.
Gaskiya Da Rikon Amana Da Kuma Tsoron Allah Ne Mafita – Inji Limamin Gajuna
“Muna jajantawa ‘yan uwa da al’ummar da wannan musiba ta shafa. Allah ya mayar musu da abin da suka rasa, ya kuma ba su juriyar wannan kaddara. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya kare gaba, ya sa karshen wannan bala’i ya zamo albarka gare su.”
Sarkin Jinkan ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga dukkan hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen gyaran da kula da magudanan ruwa a fadin kasar nan, musamman a jihohin da ambaliya ke yawan faruwa.
“Ina kira da a kara sanya ido da daukar matakai na gaggawa domin tabbatar da an tsaftace magudanan ruwa, tare da dakile duk wata gini ko cikas da ke hana ruwa wucewa yadda ya kamata. Wannan ne kadai hanyar da za a kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu daga aukuwar irin wannan bala’i nan gaba,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da ma’abota jin kai da su kai dauki cikin gaggawa ga wadanda suka shiga cikin wannan hali domin rage musu radadin da suke ciki.
Ambasada Abba Alra-iwas ya kammala da addu’ar fatan zaman lafiya da kariya daga irin wannan annoba ga dukkan al’ummar Najeriya da Afirka baki daya.
