News
Falalar Layya Da Sharudɗanta: Tattaunawa Da Imam Bello Mai-Iyali
Layya na daga cikin manyan ibadu da Musulmi ke gudanarwa a lokacin Babbar Sallah. Wannan ibada ce da take da tushe daga Annabi Ibrahim (A.S), wadda kuma Allah ya yi umarni da ita cikin Alƙur’ani mai girma.
A zantawarsa da PREMIUM TIMES, Imam Bello Mai-Iyali, wani fitaccen malami a Abuja, ya bayyana cewa Layya sunnah ce mai ƙarfi, wadda Manzon Allah (SAW) ya yi, kuma ya karfafa wa al’umma yin ta.
Indiya Ta Tabbatar Da Asarar Jiragen Yaƙi A Arangamar Da Ta Yi Da Pakistan
“Allah ya ce: ‘Ka yi sallah ga Ubangijinka, ka yi yanka.’ Wannan umarni ne kai tsaye da ke nuna muhimmancin Layya.”
Falalolin Layya
Imam Bello ya bayyana wasu daga cikin alheran da ke tattare da Layya kamar haka:
Babu wani aiki da yafi falala a ranar Sallah kamar Layya.
Aikin ibada ne da Allah yafi so a wannan rana.
Daga kowane silin gashin dabbar Layya akwai lada.
Layya tana nuna godiya da biyayya ga Allah.
Ta kusantar da bawa da Ubangijinsa.
Ta raya sunnonin annabawa.
Tana taimakawa wajen ciyar da iyalai da tallafa wa talakawa da miskinai.
Dabbobin Da Ake Iya Yi Layya Da Su
Layya tana buƙatar dabba mai cikakken lafiya. Imam Bello ya bayyana cewa ba a yarda a yi Layya da dabbar da ke da aibi ba, kamar:Mai ido ɗaya,Gurguwa,Mai karyayyen kaho,Tsohuwa mai rauni,Dabba busasshiya ko ta rame.
Shekarun da ake buƙata ga kowane nau’in dabba sune:Rago/Tumaki: shekara ɗaya, Akuya/Awa: shekaru biyu.
Saniya: shekaru uku., Rakumi: shekaru biyar.Ya ƙara da cewa: “An fi son babban rago fari, mai lafiyayyen jiki da kyau.”
Mutum bakwai na iya haɗa kuɗi su yi Layya da saniya ko rakumi, amma ba su da damar yin haka da raguna ko awaki.
Lokacin Yanka Da Ka’idojin Layya
Ana yanka Layya ne bayan sallar Idi, bayan liman ya gama nasa. Idan hakan bai samu ba, ana iya yanka a rana ta biyu ko ta uku kafin faduwar rana.
Sharudɗan Mai Layya sun haɗa da:
1. Daga farkon Dhul-Hajj, wanda ke da niyyar Layya ba zai aske gashi ko yanke ƙumba ba har sai ya yanka.
2. Ana son mutum ya yanka da kansa. Idan ba zai iya ba, sai ya wakilta wani.
3. A lokacin yanka, a kwantar da dabbar a gefen hagu, a ce:
“Bismillahi, Allahu Akbar, Allahumma hadha minka wa laka, Allahumma hadhihi anni wa an ahli baiti.”
4. A tabbatar da tsarkin zuciya, a wanke wuka kafin amfani da ita.
5. Za a iya yin Layya da niyyar iyaye ko dangin da suka rigamu gidan gaskiya.
6. Halas ne mutum ya ci bashi don siyan dabbar Layya idan yana da damar biya cikin sauƙi.
7. Babu laifi a ba wanda ba Musulmi ba kyautar nama ko sadaka.
8. Haramun ne a sayar da wani abu daga cikin dabbar Layya, kuma haramun ne a biya mai fida daga cikin naman.
A karshe, Imam Bello ya yi addu’ar cewa: “Allah ya karɓi ibadunmu, ya ba mu ikon gudanar da Layya bisa ƙa’ida da biyayya. Amin.”
