Connect with us

News

Ma’aikatan Shari’a Sun Tsunduma Yajin Aiki Kan Sabon Albashi

Published

on

Kotu

Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Ƙasa (JUSUN) ta shiga yajin aiki tun daga safiyar Litinin, lamarin da ya janyo tsaikon harkokin shari’a a manyan kotunan tarayya da ke fadin ƙasar.

Tun daga sassafe, ma’aikatan shari’ar da ke ƙarƙashin reshen Kotun Tarayya sun toshe ƙofofin shiga kotuna, inda suka hana alkalai, lauyoyi, ma’aikata da sauran masu hulɗa da kotu shiga harabar gine-ginen shari’a.

Advertisement

‎Ta Yaya Zuciyarka Za Ta Samu Kwanciyar Hankali Da Wahala?

Yajin aikin na zuwa ne sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da kuma biyan alawus-alawus na ma’aikata, kamar yadda wata sanarwa da JUSUN ta fitar ta bayyana.

A Babban Kotun Tarayya da ke kan titin Shehu Shagari a birnin Abuja, an rufe ƙofofi gaba ɗaya. Haka nan an rufe Kotun Ɗaukaka Ƙara da Babbar Kotun Abuja (FCT High Court) da ke Maitama, inda ma’aikata suka hana kowa shiga ciki.

Advertisement

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 30 ga Mayu mai ɗauke da sa hannun sakataren riƙo na ƙasa, M. J. Akwashiki, an umarci shugabannin JUSUN a fadin ƙasa da su umurci mambobinsu da su zauna a gida daga ƙarfe 12 na dare ranar Lahadi, 1 ga Yuni.

Sai dai JUSUN ta bayyana cewa ma’aikatan da ke ƙarƙashin Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) da kuma Kotun Koli ba su shiga cikin yajin aikin ba. Joel Ebiloma, mai magana da yawun ƙungiyar, da Danladi Nda, shugaban reshen Kotun Koli na JUSUN, sun tabbatar da hakan a ƙarshen mako.

Advertisement

Yanzu haka, an dakatar da duk wasu shari’u da ake gudanarwa, lamarin da ke barazana ga tafiyar da adalci da kuma yanke hukunci a kan lokaci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending