News
Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno
Daga maryam bashir musa
Yan Kungiyar Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Gubio dake jihar Borno inda suka yi awon gaba da Likita daya tilo dake garin, Geidam Bulama.
Mazauna garin sun bayyana cewa yan ta’addan sun dira garin ne cikin motar Hilux da babura kuma suka tafi gidan Likitan kai tsaye misalin karfe 2 na dare.
Sun kara da cewa yan bindigan basu dauki komai ko kashe kowa ba, Likitan kawai suka dauke.
Bayan mintuna 30 da dauke Likitan, yan bindigan suka dawo suka bankawa gidaje 74 wuta, amma ba’ayi rashin rai ba.
Yace: “Gidan Likitan bai da nisa ga hedkwatar yan sanda da kuma barikin Sojoji dake cikin garin Gubio.
Abin takaici ne lamarin tsaro ya fara tabarbarewa a Guno, mun fara samun hare-haren Boko Haram.”
Shugaban karamar hukumar Gubio, Bukar Zulum Zowo, ya tabbatar da labarin amma yace ba yan ta’addan bane suka bankawa gidaje wuta ba, yace gobara ce.
Yayinda aka tuntubi kwamishanar lafiyar jihar, Mrs Juliana Bitrus, ta bayyana cewa: “Lallai na samu labari da safen nan cewa an sace Dakta Bulama. Muna iyakan kokari da hukumomin tsaro don ceto shi.”
