News
Sheikh Indabawa Ya Bukaci Al’umma Da Su Kare Kansu Kafin Su Shiga Jimamin Jinkirin Jami’an Tsaro.
Shehin malamin addinin Musulunci, Sheikh Umar Ibrahim Indabawa, ya shawarci al’umma da su daina jiran jami’an tsaro su kawo dauki kafin su kare kansu da iyalansu daga barazanar ‘yan ta’adda da sauran bata-gari.
Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin hudubar Sallar Layya da ya gabatar a masallacin Darul Hadith da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano.
Ya ce abubuwa da dama da ke faruwa a yau sun nuna cewa matsalolin tsaro sun fi karfin jami’an tsaro kadai, don haka ya kamata kowa ya dauki matakin kare kansa.
“Yanzu abin takaici ne ka ga ana kai wa mutum hari, amma maimakon jama’a su taimaka masu, sai dai su tsaya suna kallo har a yi galaba a kansu. Wannan rashin kishin juna ne,” inji Sheikh Indabawa.
Ya ce mutane da dama sun kasa fahimtar cewa kare kai da iyali da dukiya a lokacin hari na iya zama sanadin samun shahada idan mutum ya rasa ransa.
“Wasu na jin tsoron kada a kashe su, sai su hakura da taimaka wa ‘yan uwansu, su bar su a hannun mugaye. Amma su sani, kowa hakan na iya faruwa da shi a kowane lokaci,” inji shi.
Shehin malamin ya kuma bada misali da yadda kananan yara ke fito da makami a bainar jama’a suna kwace wayoyi da jakunkuna, amma kowa ya zama tamkar kallon wasan kwaikwayo kawai yake yi.
Ya ce lokaci ya yi da al’umma za su farka, su hada kai da jami’an tsaro wajen kare kansu da muhallansu.
“Muna bukatar mu taimaka wa kanmu, mu tashi tsaye da kishin kai da na kasa. Wannan ba ya nufin a daina bin doka, amma a daina zama shiru ko shakka a lokacin da ake bukatar daukar mataki.”
Sheikh Indabawa ya kara da cewa, “Idan muka kalli tarihin Annabawa da Sahabbai, za mu ga irin yadda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare al’umma da neman ‘yanci.”
Ya kammala da kira ga al’umma da su kasance jarumai, su dauki matakin kare kansu da iyalansu, domin hakan ne zai sa Allah ya yi alfahari da su a ranar alƙiyama.
