Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Yabawa Hukumomin Agaji Bisa Dakile Yiwuwar Fashewar Tankar Mai A Titin Gwarzo

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba da gudunmuwar da hukumomin bayar da agajin gaggawa suka yi, wadanda suka yi nasarar dakile yiwuwar fashewar wata tankar man fetur a hanyar BUK zuwa Gwarzo ranar Laraba.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da mahadar sakatariyar hukumar NYSC, inda wata tankar dakon man fetur ta burma rami lokacin da take kokarin shiga gidan mai, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar gobara a yankin.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Taya Sabon Shugaban Hima FM Alh Isma’il Yusuf Makwarari Munar Kama Aiki

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana matukar godiya ga hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) RS1.2 Kano, hukumar kashe gobara ta tarayya, kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) bisa gaggarumar rawar da suka taka.

Gwamna Yusuf ya yaba da hadin gwiwa a tsakanin hukumomin wajen dakile faruwar hatsari ko Wani iftila’i.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga direbobin tankar mai da masu aikin mai da su kiyaye ka’idojin kariya a lokacin da ake yin lodi da sauke kaya domin kaucewa hadurra a nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending