News
Amurka Na Neman Nisanta Kanta Daga Aikin Gabagadin Kaiwa Iran Hari Da Isra’ila
Gwamnatin Tarayyar Amurka ta nesanta kanta daga harin da Isra’ila ta kai wa Iran da safiyar Juma’ar nan, lamarin da ya kara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban kasar Amurka na wancan lokaci, Donald Trump, ya bayyana cewa ya samu labarin shirin harin tun kafin Isra’ila ta aiwatar da shi, sai dai ya jaddada cewa Amurka ba ta da wani hannu cikin lamarin.
Usman Alhaji Na Neman Komawa Siyasa Ta Hanyar Farfaganda — Cewar Kungiyar NDWT
Trump ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana cewa, “Na san da harin kafin a kai shi, amma dai wannan aikin Isra’ila ne kadai, ba na Amurka ba.”
Ya kuma kara da cewa yana fatan gwamnatin Iran za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka domin rage barazanar da ke tattare da shirin ta na mallakar makaman nukiliya.
A cewarsa, “Muna fatan Iran za ta rungumi hanyar diflomasiyya maimakon takaddama da barazana.”
Tuni dai lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin kasa da kasa, musamman yadda harin ke iya haifar da sabon rikici a yankin.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin Iran ba ta fitar da wata cikakkiyar sanarwa kan harin ba, sai dai ana sa ran za ta mayar da martani nan ba da jimawa ba.
