Connect with us

News

An Raba Naira Tiriliyan 1.65 Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Kananan Hukumomi

Published

on

Kwamitin raba kuɗaɗen shiga na tarayya (FAAC) ya raba naira tiriliyan 1.659 tsakanin Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, kuɗaɗen da aka tara a watan Mayu 2025.

Wata sanarwa da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya fitar ta ce an cimma matsaya ne a taron FAAC na watan Yuni da aka gudanar a Abuja.

Masarautar Gaya Ta Sauke Alhaji Usman Alhaji Daga Mukamin Wazirin Gaya

Sanarwar wacce Mista Bawa Mokwa, daraktan hulɗa da jama’a a ofishin, ya sanya wa hannu, ta ce: “Jimillar kuɗaɗen da aka tara a watan Mayu sun kai naira tiriliyan 2.942, amma naira tiriliyan 1.659 ne aka raba.”

Ga yadda aka raba kuɗin:

Gwamnatin Tarayya: naira biliyan 538.004

Jihohi: naira biliyan 577.841

Advertisement

Kananan hukumomi: naira biliyan 419.968

Jihohin da ke da albarkatu: naira biliyan 124.076 a matsayin kaso 13%

Kuɗaɗen sun haɗa da:

Haraji: naira biliyan 863.895

Harajin VAT: naira biliyan 691.714

Harajin lantarki (EMTL): naira biliyan 27.667

Advertisement

Banbancin canjin kuɗi: naira biliyan 76.614

Rabon Haraji:

Tarayya: naira biliyan 393.518

Jihohi: naira biliyan 199.598

Kananan hukumomi: naira biliyan 153.881

Jihohin da ke da albarkatu: naira biliyan 116.898

Advertisement

Rabon VAT:

Tarayya: naira biliyan 103.757

Jihohi: naira biliyan 345.857

Kananan hukumomi: naira biliyan 242.100

Rabon EMTL:

Tarayya: naira biliyan 4.150

Advertisement

Jihohi: naira biliyan 13.833

Kananan hukumomi: naira biliyan 9.683

Rabon banbancin canjin kuɗi:

Tarayya: naira biliyan 36.579

Jihohi: naira biliyan 18.553

Kananan hukumomi: naira biliyan 14.304

Advertisement

Jihohin albarkatu: naira biliyan 7.178

Sanarwar ta ce daga cikin kuɗin da aka tara a watan, naira biliyan 111.908 aka kashe wajen biyan kuɗin tara haraji, sai naira tiriliyan 1.171 da aka ware domin tallafi da sauran ayyuka.

FAAC ta ce akwai ƙaruwa wajen samun kuɗi daga harajin kamfanoni, VAT da harajin shigo da kaya, sai dai an sami raguwar kuɗi daga harajin fetur da na lantarki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending