Connect with us

News

‎Ba Wuta, Ba Oxygen” – Iyalin Marigayiya Amina Sun Danganta Mutuwarta da Sakacin Asibitin AKTH

Published

on

A asibitin Aminu Kano likitoci suka cire min mahaifa da Jaririna ba tare da sanina ba Maimunat Ibrahim da ga Kano

Iyalin wata mata mai suna Amina Muhammad Aliyu Gumel sun zargi Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da sakaci, wanda suka ce ya yi sanadin rasuwarta bayan tiyatar haihuwa da aka yi mata.

‎ Rahotanni na nuni da cewa marigayiyar ta isa asibitin da kanta a ranar Juma’a, inda ta ce tana fama da ciwon ciki. Daga nan ne aka jefa ta cikin jinkiri da rashin tsari wajen samo jini kafin a yi tiyatar  (CS).

Advertisement

‎“An ce sai an samo jini kafin a yi CS. Daga baya suka ce ba sai jinin ba, daga baya kuma suka ce tana bukata. Komai rudani ne,” in ji mahaifiyarta, Hajiya Bilkisu Mukhtar, yayin da take magana da manema labarai.

‎Bayan kammala tiyatar, Amina ta shiga cikin hali na wahala, inda iyalanta suka ce ta kasa numfashi yadda ya kamata, amma ba a dauki matakin gaggawa ba.

Advertisement

‎Sun bayyana cewa an saka ta a na’urar oxygen da ake sarrafawa da hannu, kafin daga bisani a hada ta da oxygen concentrator, amma a lokacin babu wutar lantarki.

‎“Mun rika amfani da fankar hannu saboda zafi da wahalar numfashi. Mun nemi a kaita ICU, suka ki. Aka maida ta dakin haihuwa, duk da cewa ta haihu,” in ji mahaifiyar marigayiyar.

Advertisement

‎Amina ta rasu ne a ranar Lahadi, kwana biyu bayan tiyatar. Iyalanta sun bayyana cewa mutuwarta sakaci ne da za a iya kauce masa da kayan aiki na zamani da ingantaccen tsarin jinya.

‎Sun ce ba za su yi shiru ba, domin irin wannan lamarin yana ci gaba da janyo asarar rayuka a asibitocin gwamnati.

Advertisement

Da aka  tuntubi mai magana da yawun Asibitin AKTH, Hauwa’u Inuwa Dutse, ta ce an riga an fara gudanar da bincike kan lamarin.

‎“Mun dauki wannan batu da muhimmanci. Likitoci da sashen kula da lafiyar marasa lafiya sun fara nazarin takardun marigayiyar,” in ji ta.

Advertisement

‎Sai dai ta jaddada cewa dangi ba su da hurumin tsoma baki ko yanke hukunci kan matakan da likitoci ke dauka wajen jinya.

‎“Za mu fitar da bayani bayan an kammala bincike. Idan akwai wani gyara ko kuskure, za a dauki mataki,” in ji ta.

Advertisement

‎Lamarin na Amina ya sake jaddada matsalolin da suka dabaibaye fannin lafiya a Najeriya, musamman a asibitocin gwamnati, ciki har da karancin kayan aiki, rashin wuta da tsarin jinya maras tabbas.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending