News
Ba Mu Warware Rawanin Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Ba —Gwamnan Adamawa
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba ta tube rawanin Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, kamar yadda ake ta yadawa ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Yola, babban birnin jihar, jim kadan bayan da sabuwar dokar da ke tsara masarautun jihar ta samu amincewar majalisar dokokin jihar.
Albashin N70,000 Ba Ya Iya Daukar Nauyin Ma’aikatan Najeriya — NAFOHEADS
A cewar Fintiri, dokar ba ta da alaka ko nasaba da tube wani mukami na sarauta, musamman ma na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
“Ina so in bayyana wa jama’a cewa wannan doka ba ta taba mukamin Wazirin Adamawa ba. Ba ta ambaci Atiku Abubakar ko wani mukaminsa na gargajiya ba. Yana da kyau a daina yada jita-jita marasa tushe da ke nufin tayar da zaune tsaye,” in ji Fintiri.
Tun bayan amincewar majalisar jihar da dokar, wasu rahotanni sun fara yaduwa a kafafen yada labarai da ke cewa an tube rawanin Atiku Abubakar, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da muhawara a tsakanin jama’a.
Gwamna Fintiri ya ce sabuwar dokar ta masarautun jihar Adamawa an samar da ita ne domin daidaita harkokin sarautu da tabbatar da adalci da gaskiya wajen gudanar da mulkin gargajiya a jihar.
Ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi wata doka da nufin bata wani mutum ko kabilar wani yanki ba.
“Muna girmama dattawan mu da kuma wadanda suka bayar da gudummawa wajen ci gaban jihar Adamawa da Najeriya baki daya,” in ji Gwamna Fintiri.
Har yanzu dai masarautar Adamawa ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba, sai dai ana ci gaba da samun martani daga bangarori daban-daban kan dokar.
