Connect with us

News

‎Matasa Maza Na Kara Shiga Sana’ar Gashin Masara A Kano ‎

Published

on

Masu gasa masara

Sana’ar gashin masara wadda aka fi sanin mata na gudanar da ita, musamman daga yankunan Kudancin Najeriya, na ƙara samun karɓuwa a tsakanin matasa maza a jihar Kano, tare da alamun cewa mazan na ƙoƙarin mamaye harkar gaba ɗaya.

‎Binciken da Jaridar INDA RANKA ta gudanar ya gano cewa samari da dama sun fara komawa sana’ar gashin masara a matsayin hanyar samun halal da dogaro da kai a tsakanin al’umma.

Advertisement

Tsohon Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti Zai Yi Zaman Gidan Kaso Na Shekara Guda

‎A titunan Kano kamar na jami’ar BUK, Sabon Titi, Hotoro da Zaria Road da kuma kan tituna da lunguna na birnin Kano, ana ganin samari na zaune a bakin titi suna gasa masara da sayarwa ga masu wucewa da masu yawo a kasuwanni.

‎wani  matashi da ke gudanar da sana’ar a kan titin BUK, ya shaidawa wakilinmu cewa kullum sai ya je Kwanar Ƙarfi a ƙaramar hukumar Kura domin siyan masara buhu-buhu.

Advertisement

‎“Ina dawo da ita nan na ke gasa ta a bakin titi. Ina samun riba mai kyau, kuma wannan sana’a ce mai sauƙi da taimakon kai. Ba na jiran gwamnati ko wani aiki,” in ji shi.

‎Ibrahim, wani matashi daga Tudun Yola da ke cikin birnin Kano, ya bayyana cewa gashin masara shi ne tushen rayuwarsa tun bayan da ya kammala sakandire.

Advertisement

‎“Wannan sana’ar ita nake rufe kaina asiri da ita. Ina siyan masara, ina gasa wa, kuma daga abin da nake samu, ba wai kawai na ke kula da kaina ba, har da taimakawa iyayena a gida,” in ji shi cikin farin ciki da alfahari.

‎Masana na nuni da cewa sauyin rayuwa da matsin tattalin arziki sun sa mutane komawa kowace irin sana’a muddin za ta samar da abin dogaro da kai.

Advertisement

‎“A yau babu wata sana’a da za ka ce na mata ce ko na maza. Lokacin da muke ciki ya nuna cewa sana’a ba ta da jinsi. Mutum dai ya nemi halal

‎Masana harkar tattalin arziki na ganin hakan a matsayin ci gaba, domin yana rage zaman banza da yaɗuwar laifuka, tare da ƙarfafa gwiwar matasa wajen ganin suna aiki da hannunsu maimakon jiran aikin gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending