News
Yan Sanda Sun Haramta Gangamin Murnar Haihuwar Peter Obi A Kaduna
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana haramta wani gangami da magoya bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, suka shirya domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce rundunar ta samu ingantattun bayanan sirri da ke nuna cewa akwai barazanar tsaro da ke tattare da wannan gangami.
Rashin Gaskiya A Ka Ragal Mulki: EFCC Na Binciken Gwamnoni 18 Masu Ci — Olukoyede
Ya ce rundunar ba ta hana jama’a gudanar da bukukuwa ko gangami na siyasa ba tare da izini ba, sai dai akwai dokokin da ya wajaba a bi domin kauce wa rikice-rikice da barazana ga zaman lafiya.
“Rundunar ‘yan sanda na girmama ‘yancin kowane ɗan ƙasa na bayyana ra’ayi da gudanar da taro cikin lumana, amma wannan lamari yana da sarkakiya duba da rahotannin sirri da muka samu,” in ji DSP Hassan.
A cewar sanarwar, bayanan sirri sun nuna cewa wasu bata-gari na shirin amfani da gangamin domin tayar da zaune tsaye a wasu sassa na jihar, lamarin da ke iya janyo tashin hankali da rugujewar doka da oda.
Bugu da ƙari, rundunar ta bayyana cewa a ranar da aka tsara gudanar da gangamin, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na da jadawalin gudanar da zabukan fidda gwanin wasu jam’iyyun siyasa, inda suka riga suka sanar da jami’an tsaro bisa tanadin doka.
“Wannan taro da ake shirin yi zai yi karo da wasu muhimman wurare da aka ware don zabukan fidda gwani, kuma hakan na iya haddasa cunkoso, rikici da barazana ga lafiyar al’umma,” in ji shi.
Don haka, rundunar ta shawarci magoya bayan Peter Obi da su dakatar da duk wani taro ko gangami da suka shirya, tare da neman su bi doka da oda wajen gudanar da murnar zagayowar ranar haihuwar shugaban nasu.
DSP Hassan ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakan doka kan duk wanda ya karya wannan umarni, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.
Ya kuma gode wa jama’a bisa hadin kai da fahimta da suke bai wa jami’an tsaro a kokarin tabbatar da doka da oda, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da gajiyawa ba.
