Connect with us

News

Trump Zai Gana Da Putin a Birnin Alaska

Published

on

images

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birinin Alaska na Amurka a ranar 15 ga watan Agusta.

Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ganawarsa da Putin gagaruma ce kuma za ta gudana ne a ranar Juma’a mai zuwa a Alaska.

Advertisement

Mun Yi Kuskure’: WAEC Ta Fadi Abin Da Ya Jawo Dalibai Suka Fadi Jarabawar 2025

Babu wani cikakken karin bayani kan ganawar a sanarwar ta Trump, amma dai ana ganin batun tsagaita wuta a yakin Rasha da Ukraine ne zai kasance maudu’i.

Tun da farko a ranar Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da shirin ganawa da Trump kan yaƙin Ukraine, inda ya ce ya na ganin Hadaddiyar Daular Larabawa ce za ta kasance mai masaukin manyan bakin biyu.

Advertisement

An shafe sama da shekara uku ana gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine kuma Trump ya sha nanata burinsa na kawo ƙarshen yakin cikin gaggawa.

A martaninsa, shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya fada cewa Ukraine ba za ta yi wa kundin tsarin mulkinta karan tsaye ba a kan batutuwan yankuna. Zelenskiy ya ce Ukraine ba za ta amince ta sallama yankunanta ga ‘yan mamaya ba.

Advertisement

Shugaban na Ukraine ya fadi haka ne a matsayin martani ga sanarwar Shugaban Amurka Donald Trump ta ganawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

Zelenskiy ya ce Ukraine tana shirye don samun mafita da za ta kawo zaman lafiya amma ba sallama yankunanta ba. Ya kara da cewa duk wata mafita da za a cimma ba tare da Kyiv ba, to mafita ce da ta saba wa zaman lafiya.

Advertisement

 

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending