Connect with us

News

‎Gwamnatin Gombe Zata Kirkiri Sabbin Kananan Hukumomi Guda  13

Published

on

images

Gwamnatin Jihar Gombe ta gabatar da kudirin kafa sabbin kananan hukumomi 13 ga Majalisar Dokokin Jihar, domin ƙarfafa tsarin mulki da bunƙasa ci gaban al’umma. Wannan kari ne a kan kananan hukumomi 11 da ake da su a halin yanzu a fadin jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Laraba, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin sauƙaƙa gudanar da mulki tare da magance matsalolin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗi, musamman a yankunan karkara da ke fama da kalubale na tsaro da cigaba.

Advertisement

Aikin Jarida Na Bukatar Gogewa Da Kwarewa – Gwamnatin Kano

Ga jerin sabbin kananan hukumomin da za a kafa tare da hedikwatocinsu:

1. Akko Arewa – Amada

Advertisement

2. Akko Yamma – Pindiga

3. Balanga Kudu – Bambam

Advertisement

4. Billiri Yamma – Tal

5. Dukku Arewa – Malala

Advertisement

6. Funakaye Kudu – Tongo

7. Gombe Kudu – Bolari

Advertisement

8. Kaltungo Gabas – Wange

9. Kwami Yamma – Bojude

Advertisement

10. Nafada Yamma – Birin Fulani

11. Pero-Chonge – Filiya

Advertisement

12. Yamaltu Gabas – Hinna

13. Yamaltu Yamma – Zambuk

Advertisement

Misilli ya ce sabbin sassan gudanarwar za su yi aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, bisa tanadin dokar Masarauta ta Jihar Gombe da aka yi wa kwaskwarima, don wanzar da zaman lafiya da inganta tsaro.

Haka zalika, kudirin ya tanadi kafa kwamitocin wucin gadi da za su rika gudanar da harkokin kowane sabon yanki, har zuwa lokacin da za a gudanar da zabukan kananan hukumomi.

Advertisement

Gwamna Yahaya ya yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar da ta baiwa kudirin gaggawa da muhimmanci, yana mai cewa wannan shiri ya yi daidai da manufarsa ta aiwatar da mulki ga jama’a, ƙara samar da ayyukan yi, da kuma inganta dimokaradiyya da haɗin kai a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending