Connect with us

Politics

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano

Published

on

DAGA AUWALU ANWAR

“Alakar Kwankwasiyya da NEPU ko PRP ita ce kwaikwayon sanya jar hula, kawai.”

—Wani Dattijon Kwankwasiyya.

Daga Siyasar Akida Zuwa Kasuwancin Siyasa

A wannan watan, shekaru saba’in da biyar da suka wuce, gagarumin al’amari ya afku a Sabongari, Kano: kafa Jam’iyyar ‘Yan Arewa Masu Akidar Cigaba (NEPU) Sawaba da wasu samari takwas masu kishin kasa suka yi. Ranar 8 ga Agusta 1950, Abba Mai Kwaru da Bello Ijumu da Baballiya Manaja da Musa Kaula da Abdulkadir Danjaji da Garba Bida da Mudi Sipikin da kuma Magaji Dambatta suka haďu a gidan Bello Ijumu, mai lamba 9, a Titin Ibadan a Birnin Kano, don kafa jam’iyyar da za ta kalubalanci zaluncin mulkin hadin guiwar masarautun gargajiya da ‘yan mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya.

NEPU ba jam’iyyar siyasa ce ba kawai; wani gangamin ne na masu akidar burin ‘yantar da Talakawa daga zaluncin da ake yi musu, bisa jajircewar gyara tsarin masarautun gargajiya a Arewacin Nijeriya da samar wa kasa ‘yanci. Duk da NEPU jam’iyyar Lardin Arewa ce, waďanda suka kafa ta sun kasance masu hangen nesa da kishin kasa.

Advertisement

Lokacin kafa ta da mahangar da take wakilta, sun wajabta a yi zurfin tunani game da yanayin da shugabancin siyasa ya tsinci kansa a Kano. Mafi cancantar mubaya’a ga cikar NEPU shekaru saba’in da biyar, ita ce a yi karatun ta-natsu game da rugujewar tsarin sahihin shugabanci, maimakon a bata lokaci ana ta biki cike da hargowa da hayaniya maras amfani.

Ta wadanne hanyoyi mafi shaharar kungiyar siyasa a Kano, Kwankwasiyya, ta haďu da, ko ta kauce wa akida da manufofin NEPU Sawaba wadanda aka san Kano bisa turbarsu? Ta yaya aka maye gurbin dabarun gwagwarmayar tabbatar da adalci, tsarkake akida da kawo daidaito a cikin al’umma da siyasar tumasanci, bautar ganin ido, da baje kolin kasuwancin siyasa?

Wannan sharhi ya yi bayanin harkokin siyasar da ake ciki da tsarin tafiyar da shugabancin da ya biyo bayan zamanin NEPU a Kano, musamman yadda siyasar akida ta zakuda wa kasuwancin siyasa wuri ya yi zauna dirshan a tsakanin al’umma.

Ta hanyar waiwaye da hararo tarihi, sharhin ya tattauna yadda aka gurbatar da siyasar sadaukar da kai ta zama siyasar saye da sayarwa har aka samu bunkasar Rabiu Musa Kwankwaso a fagen siyasar Kano. Bugu da kari, an bayyana illolin da suke tattare da irin wannan mummunan sauyi ta fuskokin siyasa da tattalin arziki da zamtakewa. Sharhin ya yi kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a cikin al’umma don kowa ya kawo tasa gudummawar har a farfado da kyakkyawar siyasar akida irin wadda tarihin NEPU da PRP ya shimfida a Kano.

NEPU: Mai Tarihin Ceton Al’umma

Manufofin NEPU da aka bayyana a Kudurin Sawaba na 1951 su ne tubalan da aka gini akidar ma’abota siyasar gwagwarmaya da kawo sauyi a Arewa. Manufofin sun kuduri niyyar:

Advertisement

1. Wargaza halascin mulkin gado kamar yadda tsarin Masarautun Gargajiya ya tanada;

2. Fahimtar tare da bayyana rashin jituwar rundunar kawancen ‘yan koren Turawa da talakawa a matsayin yaki tsakanin azzalumai da abin zalunta;

3. Dimokuradiyyantar da hukumomin mulki su kasance makaman ceto al’umma;

4. Kalubalanci zaluncin sarakuna ta hanyar wayar da kan al’umma su rungumi matakan juyin juya-hali;

5. Shimfida sabuwar akidar mulki wadda za ta tabbatar da adalci da ‘yanci da kare mutuncin dan’adam.

Kwararar akidar NEPU da Jam’iyyar Ceton Al’umma (PRP), musamman a Karkashin jagorancin ma’abocin ilimi da da’a irin Malam Aminu Kano, ta dasa saiwoyin siyasar gwagwarmayar kawo gyara da sauyi don tabbatar da adalci. Ajiye aikin Aminu a Oktoban 1950, don kalubalantar cin hanci da rashawa da wariya, da ci da gumin wani, yadda tsarin Masarautun Gargajiya ke tafiya; daura yakin murkushe zaman ta-ci-barkatai da al’umma ke ciki ne. Tarihin siyasarsa cike yake da mutunci, mahawarar ilimi, da neman daidaiton al’umma; wadannan abubuwan ne suka haifar da akidar siyasar da Kano ta taso a cikinsu shekaru aru-aru da suka

Advertisement

A Jumhuriya ta Biyu, PRP ta bunkasa ayyukan NEPU har gaggan masu ilimi irin su Chinua Achebe da Wole Soyinka da Bala Usman suka rungume ta. PRP ta fadada harkokin tallafawa raunana, da yin tasiri ga dubban mutane har suka shiga siyasa, da tabbatar da Nijeriya a matsayin kasa mai cikakken ‘yanci maimakon ‘yar koren Turawan Yamma da Amerikawa. Kirayen PRP ga al’umma a fili yake: siyasa ba rumfar saye da sayarwa ba ce a kasuwa. Siyasa fagen dagar kare mutuncin dan adam ce.

Ta’adin Sojoji ga Siyasar Akida

Farmaki ga siyasar akida ya faro ne a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida (1985-1993). Ta hanyar tursasa wa mutane shiga jam’iyyu biyun da soja ya kafa: Jam’iyyar Masu Sassaucin Ra’ayi (NRC) da Jam’iyyar ‘Yan Gaba-dai-gaba-dai (SDP), Babangida ya tumbuke jijiyoyin siyasa daga hurumin al’umma. Wadannan jam’iyyun soja sun kasance masu kishin ruwan sahihiyar akida, kuma an samar da su don su hade kawunan masu ido da tozali wuri guda, maimakon bunkasa harkokin dimokuradiyya.

Makircin sojoji na kwance auren da yake tsakanin siyasa da al’umma ya haifar da mummunan tsarin gina dillalan siyasa da biyayyar kudi hannu da bautar gumakan siyasa masu dauke da sunan shugabanni ba bisa cancanta ba. Zakudawar jama’a daga bangaren siyasar akida zuwa dandalin kasuwancin siyasa ba bakatatan ya afku ba, tsararren lamari ne. Bangarori da jami’an tafiyar da harkokin jam’iyya suka kasance wulakantattu, gatanci da son kai suka maye guraben akida da cancanta. Don haka, kamfen a siyasa ya koma ciniki da kasuwanci a maimakon yunkurin kyautata rayuwar al’umma da gina kasa.

Kano, wurin da ya kasance cibiyar akida da yunkurin tabbatar da adalci a tarihin siyasar Arewacin Nijeriya, ya rikide zuwa dandalin baje kolin kasuwancin siyasa. Nan da nan sai wasu irin shugabannin siyasa, barbarar yanyawa suka bullo, ba ta hanyar jajircewa bisa akida da sadaukar da kai ba; sai ta hanyar tsananin son kai da hadamar mulki, da damfarar siyasa. Sai kararrawar gwanjon mukaman jam’iyya da na gwamnati, ga masu kudi hannu ta binne kirarin shelar yunkurin ceton al’umma da jarumtaka. Nan da nan sai ya kasance mafiya muhimmanci da dacewa a harkokin siyasa ba su ne wadanda suke da kyawawan halaye ba, su ne masu hannu da shuni ko ‘yan lele.

Taka Rawar ‘Yan Uku: Shekarau da Ganduje da Kwankwaso

Advertisement

A tafiyar da harkokin siyasa a Kano, bayan shudewar PRP, mutane ukun da suka fi sauran ‘yan siyasa tasiri har tsawon shekaru ashirin da biyar su ne: Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Kowannensu ya yi zango biyu (shekaru takwas) a karagar mulkin Jihar Kano. A wuyan gabadayansu alhakin gurbacewar siyasar Kano, daga gwagwarmayar tabbatar da akidar gyaran al’umma da gina kasa zuwa baje kolin kasuwancin siyasa, ya rataya.

A ‘yan kwanakin nan, an samu tarayyar ra’ayin masu sharhi a kan harkokin siyasa, da al’amuran yau da kullum, kwararru da masana, kamar tsohon Mai Bayar da Shawara ta Musamman kan Harkokin Addini a zangon farko na mulkin Kwankwaso (1999-2003), wanda ya sake rike mukaman Kwamishina a Ma’aikatun Ilimi Mai Zurfi da Harkokin Addini a gwamnatin Ganduje (2019-2023), Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) da Shugaban Kungiyar Gamayyar Malamai ta Jihar Kano, Ibrahim Khalil, cewa alhakin cigaban gurbatar tarbiyyar matasa da rugujewar jam’iyyun siyasarmu, a matsayinmu na al’umma, kacokan ya rataya a wuyan wadannan hamshakan ‘yan uku, saboda rawar da suka taka ko suke takawa har yanzu.

Tabbas, kowane dayansu yana da irin nasa gararin a matsayinsa na mutum, ko na dan siyasa. A daidai nan, zan bayyana yadda jama’a suke kallon alakarsu da tabarbarewar harkokin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a Jihar Kano. Zan kuma fadi fahimtata da tasirin ayyuka da tsare-tsarensu na siyasa ga al’umma.

Don kore shakka, ba ni da matsala da kowane dayansu. A gaskiya, ina da kyakkyawar dangantaka da Ganduje. Ni da Shekarau muna matukar mutunta juna. Dabarun Kwankwaso na zaburar da mutane da cafke su gam-gam da rike akalar biyayyarsu, na ba ni sha’awa kwarai da gaske. Duk da haka, kaunar Kano da kasancewa dalibin tarihi sun rinjayi sauran al’amura masu kai-kawo a zuciyata.

 

Ibrahim Shekarau

Advertisement

Mutane na daukar Shekarau mai karancin laifi a kan sauran. Ba shi da dagawa. Bai yi girman kai ba ko lokacin da yake gwamna. Shigarsa ofis ba ta haukata shi da giyar mulki ba. Ba mai kallon sa a matsayin 6arawo. Ba a zarge shi da sace kudaden Kananan Hukumomi kai-tsaye ko ta dabarun kirkirar asusun hadin gwiwar boge don manyan ayyuka na musamman ba.

Duk da haka, kasancewarsa da ko uban Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS) a lokaci mai tsawo; kuma wanda guguwar farfado da Shari’a ta wurgo shi kan kujerar gwamna, sabanin mutumin da ya gada mai yi wa harkar farfado da Shari’ar Musulunci rikon sakainar kashi, a zamaninsa an ga gaggawar kokarin ‘Musuluntar’ da tsarin tafiyar da gwamnati da hukumominta. Shekarau ya zurarar da lalitar jama’a wurin biyan bukatun kungiyoyin addini da na mutane masu kai-kawo da siffar wakilcin addini. Dauraye ayyukan siyasar Shekarau da ruwan addini ya sa wasu zaton a fannin addini ya samu digirinsa maimakon lissafi.

Duk da tsantseninsa na rike amanar dukiyar al’umma, ana zargin sa da rauni wurin kare martabar asusun gwamnati. Bai kasance mai sa cikakken ido da tsawatarwa ko hukunta mabarnata a cikin ma’aikatansa ba; duk da an zargi wasu da tabargaza da ha’inci.

Haka kuma, ‘yancin da ya ba kananan hukumomin, lokacin mulkinsa, ya tona asirin zurfin almubazzaranci da kwarewar cin rashawar jami ansu.

A gaskiya Shekarau bai yi nasarar gabatar da muhimman ayyukan inganta rayuwar al’umma ba a lokacin mulkinsa; hankalinsa ya fi karkata wurin kokarin ‘gyaran zukatan mutane’ ko ‘a daidaita sahu, Ya kirkiri hukumomi barkatai irin su Hukumar Shari’a da Hukumar Hisbah da sauransu a yunkurinsa na neman cim ma wannan buri.

Duk da rauninsa a harkar shugabanci, Shekarau ya fahimci bambance-bambancen da ke cikin al’umma kuma ya yi kokari wurin kwatanta adalci da sasanci a tsakaninsu. An samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamaninsa maimakon zaman dar-dar da ake danganta Kano da shi, a lokutan baya.

Advertisement

Bayan kyautata wa kungiyoyin addini, Shekarau ya ba da kulawa da tallafi mai gwaßi, masu kama da almubazzaranci, ga masarautu da sarakuna. Wannan ne ya sa Sarkin Kano, Ado Bayero, ya nada shi Sardaunan Kano a matsayin godiya ko tukuici. Kawancensa da masarautun gargajiya ya saba wa manufofin NEPU da PRP. duk da cewa masarautun sun kasance burßushin al’ada da tarihi.

A matsayinsa na dan siyasa, Shekarau daidai yake da Kyanwar Lami: ba cizo ba yakushi; wato ba yabo ba fallasa. Ya yi cincirundon mabiya rantsattsu a baya, amma sannu a hankali ya watsa su saboda rashin ingantaccen tsarin shugabanci da yawan tsalle-tsalle tsakanin jam’iyyu a matsayinsa na jagora.

Ba a dauke shi mutum kaifi daya ba. Kuma ana zargin sa da yin alkawura masu harshen damo.

Tsirarun mabiyansa da suka rage, suna cewa babbar matsalarsa ita ce, sha’awar ya dadada wa kowa, wanda a mafiya yawan lokuta, sai ya munana wa kowa. Watakila shi ya sa yake yin alkawura wadanda ba zai iya cika su a lokutan da suka kamata ba.

Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje, a ra’ayin jama’a, shi ya fi sauran wahalar kwatance. Misali, yana da faran-faran da mutunta kowa, tamkar dillalin alewa, sai dai walwalarsa ba ta nufin labarin zuciya a tambayi fuska. Don haka wasu suke yi masa kirarin “macijin kaikayi, sari ka noke.” Mutum ne mai matukar waskiya da zilliya da zamiya. Ana zargin ya dauki yaudara da riya a matsayin farillan huldarsa da dangantakarsa ta siyasa da jama’a. Yana da hakuri, ga wayo kamar dila, gami da hangen nesa.

Advertisement

Akwai alamun bai amince da kowa ba sai kansa. A matsayinsa na jami’in gwamnati, an dauke shi tamkar wata mabu66ugar cin hanci da rashawa. Kwadayinsa na handama da wawura da babakere, ya wuce maganar hadama, ya zama tamkar wani gawurtaccen mikin mutu-ka-raba a cikin kokon zuciyarsa.

Akwai masu zargin duk wata kwangila da gwamnati ta yi a lokacinsa, daga dinka wa ‘yan jam’iyya kayan ashobi zuwa ginin gada, shi ne dan kwangilar. Misali, hotunan bidiyon da aka nuna shi yana karbar cin hancin daloli wurin wani dan kwangila, duk da ya ci gaba da karyata ingancin zargin, idan ya tabbata gaskiya ne, ba a taba samun gwamnan da ya wulakanta kansa haka ba.

Duk da zargin zarmewarsa a harkokin son zuciya, ayyukan gine-gine da gwamnatinsa ta yi ingantattu ne bisa shaidar kwararru. Wato sun saßa da ayyuka awon igiya masu muguwar tsada wadanda gwamnatin Kwankwaso ta yi.

Saboda tsananin son kansa, ya kasa rike nagartattun ‘yan siyasa masu mutunci a tawagarsa. Don haka ya gaza samun tabbataccen zatin kansa na siyasa, kuma yake rakuße cikin inuwar Kwankwaso a tsawon shekaru takwas da ya mulki Jihar Kano.

Yawancin abokan burminsa a siyasance sun kasance ‘yan jagaliyar siyasa da zauna gari banza. Mutanen da ba su iya amfanar kansu balle su amfanar da wani. Ma’aikata masu amana da ‘yan siyasa masu mutunci ba su da wata kima a gaban Ganduje, balle su sami kwarin gwiwar tafiyar da ayyukansu a tsanake.

Misali a lokacin babban zaben 2023, yaronsa da ya nada Shugaban Jam’iyyar Gamayyar ‘Yan Cigaba (APC) a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, a fili ya roki kar Allah ya kiyaye masifar da za ta tashi idan zaben gwamna ya zo. Take addu’arsa ta karbu, zaßen ya zo aka kayar da su kasa wanwar da halastacciyar kuri’a..

Advertisement

Abin mamaki, a matsayinsa na gwamnan da ya yi shekaru takwas bisa karagar mulki, kuma tsohon shugaban jam’iyyar da take mulkin kasa, Ganduje ba shi da wata tawaga muhimmiya ta ‘yan siyasa a tare da shi a Kano. Wannan ba ya nufin babu kilakin siyasa da ‘yan iska da ‘yan ta’addar da zai iya dauka haya, domin su yi masa kwangilar rashin mutunci, ko assasa mummunan tashin hankali, idan akwai bukatar hakan.

Akwai ma’aikata da ‘yan boko jingim masu takaicin irin damarmakin da Ganduje ya samu na ya gyara muhimman al’amura a Jihar Kano, ya watsar da gangan.

A cikin su ukun, ya zarta sauran ilimi; kwarewa; wayewa; dukiya da shekaru a lokacin da ya zama gwamna. Jimillar ayyukansa ba ta nuna ya fi sauran tsumma ba, balle ya kada musu kwarkwata. Biyayya ta fi cancanta samun Kyakkyawan sakamako wajen tafiyar da ayyukan siyasa da na gwamnati, a wurin Ganduje.

Abin mamaki, duk da mutane na ganin Ganduje a matsayin matsolo, akwai wasu zababbun mutanensa da abokan hulda wadanda yake yi wa aiken kudi a wasu lokuta, musamman a bikin karamar Salla da babba, na kowace shekara.

Bisa la’akari da tarihin siyasar akida da shugabancin NEPU ya dasa a Kano, mutane na cike da mamakin shin mene ne dalilin cigaban gurßacewar harkokin shugabancin siyasa a Jihar Kano?

 

Advertisement

Rabiu Musa Kwankwaso

Cikin mutane ukun da ake zargi da alhakin gurbacewar tarbiyyar matasa da zagwanyewar mutuncin siyasar akida, Kwankwaso ne kadai dirarren dan siyasar da yake ta dimbin magoya bayan da suke da tasiri a wurin iya juya akalar ko gurbata tarbiyyar siyasa a Kano.

Don haka ya zama wajibi wannan sharhi ya tattara hankalinsa a kan Kwankwaso da burin a fahimci yanayin alakarsa da tushen masifar da Jihar Kano ta fada ciki tsundum.

Yayin tattauna me ya haifar da kasuwancin siyasa har gurbatar abubuwa ta rinjayi siyasar akida a Kano, wajibi ne a yi nazarin tarihin shiga siyasar Kwankwaso, dabarunsa na samun mabiya da bunkasarsa a fagen siyasar jihar.

Shin Kwankwaso sahihin dan siyasa ne me burin gina al’umma, ko dan damfara ne, mai amfani da kidahumancin mabiyansa don ya ci da guminsu?

Amsa wannan tambaya zai fi sauki idan aka hararo yadda siyasa ta sauya kamanninta a Kano; daga gwagwarmayar ceton al’umma a karkashin jagorancin Aminu Kano, zuwa kasancewa kamfanin saye da sayarwar Kwankwaso don ya yi safarar mabiyansa, ya more ribar cinikin shi kadai, a bagas.

Advertisement

Dimbin masoyan Kano suna takaicin yadda al’muran siyasa suka tabarßare a jihar har mai ra’ayin rikau irin Kwankwaso ya samu damar kafa kamfanin siyasa mai dauke da sunansa (Kwankwasiyya); kuma yake baje kolinsa a ciki yadda ya ga dama. Ya kamata a fahimci kaurace wa siyasa da sahihan mutane masu mutunci da kyakkyawar akida suka yi, ta ba Kwankwaso damar kwakwashe matasa da hure musu kunnen su yi masa leburanci, shi kuma a matsayinsa na madugu ya dinga amshe ladan kwadagonsu. Kura da shan bugu gardi da karbe kudi!

Sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga.

Shin mene ne tarihin siyasar Kwankwaso da dabarun yakinsa, domin a fahimci yadda bunkasarsa ta juya akalar siyasar Jihar Kano maimakon kyautata akidar gwagwarmayar neman ceto al’ummar kasa zuwa fafutukar kokarin neman mulki da tara dukiya don biyan bukatar kansa.

Tarihin siyasar Kwankwaso ya fara daga zuwansa Majalisar Wakilai ta Taryya daga Mazabar Kura-Madobi-Garun Malam, a karkashin tutar SDP, a cikin Yuli na 1992. Ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar a lokacin da kujerar ta fado Jihar Kano. A 1994 ya ci zaßen kai da halinka, zuwa Taron Tattauna Tsarin Mulkin Kasa, daga Gundumar Kano Ta Tsakiya.

A 1999, ya tsaya takarar fitar da gwani a PDP don samun damar tsayawa zaßen gwamnan jiha wanda ake shirin yi. A kuri’un da deliget suka jefa, Ganduje ya yi wa Kwankwaso fintinkau.

Nan take wani abokinsa, Hakimin Gabasawa, Aminu Babba Dan Agundi, ya kawo wa Kwankwaso daukin gaggawa da haramtattun kur’un da ya kirkira na boge a Mazabar Gabasawa; don haka aka ce wai ya yi nasarar kifar da Ganduje.

Advertisement

Wannan cin amana da su Kwankwaso suka yi, ya kusa wargaza jam’iyyar PDP a Jihar Kano. Abin mamaki, sai Ganduje ya rungumi ‘kaddara domin jam’iyya ta zauna lafiya, kar a yi uwar-watsi. Halin dattakon da Ganduje ya nuna, ya janyo masa farin jini da tausayi da kauna a wurin shugabancin jam’iyyar.

Idan da gaske, yadda mutane ke zargi, Ganduje ya tafka magudin barar da su Kwankwaso a zaßen gwamna na 2019, sai a ce kwaryar da ta tafi ce ta dawo. Wato an yi ramuwar gayya, ko an yi wa wanzami jarfa.

Mafiya yawan nasarorin Kwankwaso a matsayinsa na gwamna sun faru ne a zangonsa na farko (1999-2003), wato lokacin da ya yi aiki da mutane kwararru, masu mutunci da kishi da cancanta da sadaukar da kai a cikin majalisarsa ta zartaswa. Lokacin kan mage bai waye ba.

Zangonsa na biyu da wanda yake kai yanzu na uku da sunan Abba Kabir Yusuf; ana kwatancensu da kwarewa a cikin ayyukan yaudara da damfara da cin amana da yashe asusun jama’a ta hanyar kirkiro wani haramtaccen tsarin samartakar bera mai suna: Asusun Hadin Gwiwar Gwamnatin Jiha da na Kananan Hukumomi. Mafiya rinjayen ayyukan da ake gudanarwa ta wannan asusu babu su a kasa. Don suna da layar zana. Babu wanda yake iya ganin su sai mai wankin ido, kamar Madugu da lamuntattunsa.

Cikin irin ayyukan da yake alfahari da su, wasu tun a zangonsa na farko, kamar: tituna kilo mita biyar-biyar a kananan hukumomi; sikolashif don karatu a kasashen waje: almarar tsayawa takarar shugabancin kasa; asusun hadin gwiwa don wadata asibitoci da magunguna; katafarun gadoji a cikin birnin Kano; da kafa wasu cibiyoyin ilimi na boge; misali, Cibiyar Wasanni a Kura, dukkaninsu hanyoyin sace kudaden al’umma ne kai-tsaye da rana tsaka.

Misali, kwanakin baya, tsohon Sakataren Gwamnatin NNPP a Jihar Kano, Baffa Abdullahi Bichi, ya furta cewa idan ya bude bakinsa game da sace-sacen da ake yi a wannan gwamnatin ta Kwankwasiyya sai mutanen Kano sun kori Kwankwasawa da ruwan duwatsu. Ya yi alkawarin amayar da duk abin da ya sani bisa dogaro da rubutattun bayanai idan lokacin yin hakan ya zo. Muna ji, muna gani, muna kuma saurare.

Advertisement

A zaton Kwankwaso yana da wayon da zai wofantar da hankali da tunanin kowa a kullum. Farfagandarsa ba ta hana mutane fassarar gwamnatinsa ta NNPP da sunan daular gafiyoyi ko dandalin samartakar beraye ba.

A kidahumancinsa, watakila har da jahilci, bai san kifi na ganin sa mai jar koma ba. Lallai gobe za a sha kallo, idan tarko ya kama burgu, asiri zai tonu.

Mutane da yawa sun dau Kwankwaso mai girman kai saboda zaton ya fi kowa. A gaskiya ban amince da wannan ra’ayin nasu ba.

Kwankwaso na fama da kalubalen tunanin gazajjen mutum saboda rashin cancantarsa a fuskokin shugabanci masu yawa da kuma dakikanci. Wannan dalilin ne ya sa shi karyar yana da digirin digirgir, lokacin da ya zama gwamna a 1999, Mutumin da Allah ya girmama da zama Gwamnan Kano, kuma mai cikakken hankali, ba zai shara irin wannan karyar ba don babu.

Gazawarsa, watakila da rashin samun cikakkiyar tarbiyya a kuruciyarsa, sun sa shi nishadin wulakanta muhimman mutane masu mutunci wadanda kowa ke girmamawa bisa cancanta a cikin al’ umma. Misali, ya ci mutuncin Sarkin Kano, Ado Bayero; ya yi wa Aminu Dantata rashin kunya; ya wulakanta Abubakar Rimi; ya muzanta ubansa na rana wanda ya tsamo shi yana gantali a karkara ya koya masa siyasa, Hamisu Musa; ya yi wa malaman addini ashariya wadanda suka yi tir da halayyarsa.

Ayyukan Kwankwaso na tabargaza sun zarce girman kai. Ya kamata iyalai da masoyansa su fara tunanin hanyoyin da za su bi don shawo kan al’amarin. Allah ya sa a dace. Amin.

Advertisement

Kwankwaso ne, shi kadai jal, yake da kaso mafi yawa cikin gurbacewar tarbiyyar siyasa a Jihar Kano; da raunana jam’iyyunta; da yaudarar matasanta; wanda a dalilin haka harkokin siyasa suka zama baje kolin saye da sayarwa a kamfanin Kwankwasiyya.

Idan mutane masu mutunci da amana da tunani suka kawo sabon tsari ta fuskar tsarkake harkokin siyasa da tarbiyantar da matasa sanin muhimmancin siyasar akida da sadaukarwa, share Kwankwaso da kasuwancin siyasar kamfanin Kwankwasiyya, a dandalin siyasar Kano, da yardar Allah kamar yanzu ne.

Ya kamata duk sahihan kungiyoyin matasa da jam’iyyun siyasa da daidaikun mutane masu akidar gyara kasa da gina al’umma su fahimei Kamfanin Kasuwancin Siyasa na Kwankwasiyya mallakar Kwankwaso wata guba ce da guguwar gurbatacciyar dimokuradiyya ta yaryada ta a Jihar Kano, kuma kowa ya guje ta.

Idan wannan sharhi ya sa wasu masu karatu tunani a kan zurfin gurbacewar harkokin siyasar Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano, kuma suka amince da muhimmancin a jaddada manufofin jam’iyyun NEPU da PRP, sai in yi gudar na cika burina.

NEPU! Sawaba!!; PRP! Nasara!!; Kwankwasiyya! Asara!!

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending