News
Akwai Bukatar Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Najeriya Kamar Yadda Aka Yi A Lokacin Korona Domin Magance Matsalar Tsaro – Buratai
Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da kulle iyakokin ƙasar da kuma ɗaukar matakan tsauraran tsaro domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Buratai ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Channels TV a ranar Juma’a, inda ya ce barin tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa babban haɗari ne ga zaman lafiya da ci gaban ƙasar.
Za A Fara Daure Mazan Da Ba Sa Zuwa Sallar Juma’a A Malaysia
“Akwai buƙatar jajircewar al’umma da haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa, na gargajiya da na addini domin samar da mafita kan matsalar tsaro,” in ji shi.
Ya ce tun a baya ya yi gargadin cewa za a ɗauki lokaci mai tsawo ana fama da matsalar tsaro, don haka akwai buƙatar a ɗauki matakan dogon lokaci domin magance ta.
Buratai ya kuma yi kira da a ɗauki sojoji a matsayin ginshiƙin kawo ƙarshen matsalar tsaro maimakon kallonsu a matsayin cikas.
Ya jaddada cewa haɗa ƙarfi da ƙarfi tare da ɗaukar tsauraran matakai ne kawai zai iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro a faɗin Najeriya.
