Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Cimma  Wata Yarjejeniya Da ASUU – Ministan Ilimi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin da ake yi cewa ta kulla wata yarjejeniya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), inda ta bayyana cewa duk wani takarda da aka gabatar ga kungiyar na dauke ne da shawarwari, ba yarjejeniya ba.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, inda ya yi karin bayani kan zanga-zangar da ASUU ke gudanarwa a sassan kasar nan.

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Dalibar Da Ta Lashe Gasar Turanci Ta Duniya Da Kyautar Naira 200,000

A cewarsa, gwamnatin ba za ta kulla wata yarjejeniya ta bogi ko wadda ba za a iya aiwatar da ita ba, sai dai tana da niyyar cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a harkar ilimi.

“Gwamnatin Tarayya ba ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU ba. Abin da ke akwai dai shawarwari ne da ake ci gaba da tattaunawa a kai,” in ji Ministan.

Dakta Alausa ya kara da cewa gwamnatin na ci gaba da tuntuba da shugabannin kungiyar domin tabbatar da samun mafita, tare da jaddada cewa zanga-zangar da aka gudanar kwanan nan ba za ta rikide zuwa yajin aiki ba.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending