News
Jami’an NDLEA Sun Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Kan Zargin Fataucin Miyagun Kwayoyi
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wani tsoho mai shekaru 75, Uchelue Ikechukwu, tare da wasu mutane biyar bisa zargin hada-hadar miyagun kwayoyi a wani samame da jami’anta suka kai a sassan jihar Anambra.
Rahoton hukumar ya bayyana cewa an kama tsohon ne a garin Umudioka, karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra, tare da miyagun kwayoyi masu nauyin kimanin kilo 26.7. An gudanar da samamen ne ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025.
Gwamnatin Tarayya Na Biyan ‘Yan Bindiga Kudi, Na Basu Abinci — El-Rufai
Sauran mutanen da aka cafke a jihar sun hada da Eneh Makuo, Emmanuel Chiemeli, Uwakwe Matthew, Chukwujekwu Ehirim, Ifeanyichukwu Olisa da Odoh Chukwuma, dukkaninsu dauke da miyagun kwayoyi iri daban-daban.
A wani samame daban a jihar Taraba, jami’an NDLEA sun kama wani matashi mai suna Alfa Andrew, mai shekaru 30, bayan rusa gonar tabar wiwi da ya shuka a kauyen Mayafi, karamar hukumar Sardauna. Gonar ta yi nauyin kimanin kilo 178,750 kafin lalata ta.
Hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da kai samame a jihohi daban-daban domin magance safarar miyagun kwayoyi a kasar.
