Connect with us

News

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Biyu Da Bindigar GPMG, Harsashi 1,295 A Katsina

Published

on

Machine Gun 750x430

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu bisa zargin safarar muggan makamai, inda ta kwace bindigar General Purpose Machine Gun (GPMG) da harsashi 1,295 a hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta ƙasa, DCP Olumuyiwa Adejobi, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina.

Advertisement

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ƙarin Naira Biliyan 215.3 A Kasafin Kudin Jihar 

A cewar Adejobi, jami’an tsaro sun cafke mutanen ne a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku, bayan samun sahihin bayanan sirri kan ayyukansu.

Ya bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da Abdussalam Muhammed mai shekara 25, da kuma Aminu Mamman mai shekara 23, dukkansu mazauna ƙauyen Baure na ƙaramar hukumar Safana, Jihar Katsina.

Advertisement

“Bincike kan motar Golf mai launin shuɗi da suke amfani da ita, mai lambar rijista RSH-528 BV, ya tabbatar da gano bindigar GPMG ɗaya, harsashin AK-47 7.62x39mm guda 1,063, da harsashin PKT 7.62x69mm guda 232 da aka ɓoye a cikinta,” in ji Adejobi.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna an yi safarar makaman daga Hadejia a Jihar Jigawa zuwa Safana a Katsina domin rarraba su ga miyagun mutane.

Advertisement

Adejobi ya ce waɗanda ake zargin na hannun hukuma, kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano tushen makaman da kuma cibiyoyin da suke da alaƙa da su.

NAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending