News
NBA Ta Maka Sufeto-Janar A Kotu
Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta kai ƙarar Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa sabuwar manufar da rundunar ƴan sanda ta ƙaddamar kan sabunta lasisin gilashin mota mai duhu.
Manufar, wacce aka sanar a watan Afrilu 2025, za ta fara aiki daga ranar 2 ga watan Oktoba, inda aka wajabta wa direbobi sabunta lasisin kowace shekara ta yanar gizo tare da biyan kuɗi. Sai dai NBA ta bayyana cewa tsarin ba ya da tushe a doka, yana kuma tauye ‘yancin ɗan adam tare da haifar da shakku game da gaskiya da riƙon amana.
Bayan Samun Ruwan Sama Mai Ƙarfi, Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Sabon Gargadi Ga Jama’a
A wata sanarwa da shugaban sashen Dokokin Jama’a da Cigaban Al’umma (SPIDEL) na NBA, Farfesa Paul Ananaba (SAN), ya fitar a ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ta samu hujjoji da ke nuna ana karkatar da kuɗin da ake biya zuwa wani asusun kamfani mai zaman kansa da ake kira Parkway Projects maimakon Asusun Tarayya.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa dogaro da dokar hana gilashin mota mai duhu ta shekarar 1991 ba ta dace da tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba kasancewar doka ce ta lokacin mulkin soja.
Saboda haka NBA ta roƙi kotu ta dakatar da aiwatar da manufar har sai an yanke hukunci kan ƙarar da ta shigar.
