Connect with us

News

Kungiyoyin Farar Hula 201 a Kano Sun Yi Watsi da Zanga-zangar Siyasa Kan Cin Hanci

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Wasu gungun kungiyoyin farar hula 201 a jihar Kano, ƙarƙashin inuwar Patriotic Coalition of Civil Society Organisations (PCCSOs), sun nesanta kansu daga wani abu da suka bayyana a matsayin “zanga-zangar siyasa” da wasu kungiyoyi biyar suka shirya a jihar kan batun cin hanci.

Kungiyoyin sun ce waɗanda suka kira kansu Forum of Kano CSOs Against Corruption ba a san su a cikin manyan ƙungiyoyin farar hula na Kano ba, kuma ba su da hurumin yin magana da sunan al’ummar jihar.

Advertisement

KANO: Jami’an Yan Sandan Sun Kama Mutane 9 Kan Tarzomar Da Ta Faru A Garko.

Sun kuma bayyana cewa zarge-zargen da aka yi kan wasu jami’an gwamnati ba su wuce tuhumomi ba, domin har yanzu hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC ke gudanar da bincike, kuma babu wata kotu da ta tabbatar da laifi a kansu.

PCCSOs ta ce gwamnatin Kano ta ɗauki matakai na tabbatar da gaskiya da rikon amana, ciki har da aiwatar da Treasury Single Account (TSA), bude kasafin kuɗi tare da bai wa kungiyoyi damar sa ido, da kuma kafa sassan lura da cinikayya a ma’aikatun gwamnati.

Advertisement

Kungiyoyin sun jaddada cewa suna goyon bayan hukumomin yaki da cin hanci su ci gaba da aikinsu, amma sun nesanta kansu daga duk wani yunƙuri da zai maida sunan farar hula kayan siyasa ko hanyar bata sunan mutane.

A ƙarshe, sun roƙi al’ummar Kano da su yi watsi da duk wani yunƙuri da zai kawo rarrabuwar kawuna, tare da tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kare albarkatun jama’a da inganta gaskiya domin ci gaban jihar ya kai ga kowa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending