News
Ƙungiyar Likitoci Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi Da Ta Shiga
Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta shiga, tare da umartar mambobinta da su koma bakin aiki daga yau Lahadi.
Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar da daren Asabar. Ya ce gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakan amsa wasu daga cikin bukatun da kungiyar ta gabatar.
Rashin Shugabanci Na Gari Shi Ne Asalin Matsalar Najeriya — Sarkin II
“Wasu daga cikin bukatunmu an biya su, sauran kuma gwamnati ta yi alkawarin duba su. Mun dakatar da yajin aikin a matsayin alamar kyakkyawar niyya, domin mu sauƙaƙa wa al’ummar da ke neman lafiya a asibitocinmu,” in ji shi.
Yajin aikin ya shafi ayyukan kiwon lafiya a sassa daban-daban na ƙasar, inda rahotanni suka nuna cewa manyan likitoci da sauran ma’aikatan lafiya ne suka ɗauki nauyin kula da marasa lafiya masu tarin yawa.
Sai dai, har zuwa lokacin fitar da sanarwar, ba a bayyana irin bukatun da gwamnatin
ta amsa ba.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
