News
Ba Kano ce ta fi kiwacce jiha cin jarabawar NECO a bana ba – Bincike
Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya gano cewa ba Jihar Kano ba ce ta fi nasara a jarabawar NECO da aka gudanar a bana ba.
Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar ta bana, Premium Times ta ce za ta iya tabbatarwa cewa ba jihar Kano ba ce jiha ma fi nasara ba.
Karyewar Gadar Gwangwan Na Kara Janyo Tsaiko Ga Rayuwar Al’umma
Wannan na zuwa saɓanin ikirarin da Gwamnan Kano, Abba Yusuf, Kano ya yi na cewa jihar ce mafi nasara a jarrabawar NECO ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa jihar Kano ce ta zo a matsayin “jiha mafi nasara a jarrabawar NECO SSCE ta 2025.”
Binciken na Premium Times ya ƙara da cewa kwata-kwata jihar Kano ma ba ta shiga cikin jihohi 10 da suka yi nasara ba, bal ma ta zo ne a matsayi na 29 daga cikin 37.
A ƙididdige, jihar Kano ce ta kowacce jihar faɗuwa jarabawar NECO a bana idan aka yi la’akari da yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar da kuma yawan waɗanda suka ci jarabawar.
Jihohi 10 da suka fi faɗi jarabawar NECO a Najeriya
Daga na 28 zuwa na 37.
28. Bauchi – 52.62 per cent
29. Kano – 49.84 per cent
30. Yobe – 48.13 per cent
31. Adamawa – 47.99 per cent
32. Plateau – 46.46 per cent
33. Borno – 44.72 per cent
34. Jigawa – 43.81 per cent
35. Katsina – 42.89 per cent
36. Zamfara – 42.12 per cent
37. Sokoto – 35.00 per cent
Jihohi 10 da suka fi yin nasara jarabawar NECO 2025
Abia – 83.31 per cent
Imo – 83.09 per cent
Ebonyi – 80.60 per cent
Anambra – 76.80 per cent
Bayelsa – 73.88 per cent
Delta – 73.10 per cent
Osun – 72.64 per cent
Ogun – 72.21 per cent
Lagos – 71.76 per cent
Ekiti – 68.50 per cent
