News
Stallion Times Da NUJ Sun Horar Da ’Yan Jaridu Kan Yadda Za Su Yi Amfani Da Fasahar AI
DAGA LUKMAN ABDULMALIK, JOS
Jaridar Stallion Times, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Filato sun gudanar da taron horaswa na musamman ga ’yan jaridu kan yadda za su yi amfani da Fasahar Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence – AI) ba tare da karya ƙa’idojin aikin jarida ba.
Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a haɗa ci gaban fasahar zamani da ƙa’idojin aikin jarida, domin tabbatar da cewa labarai da rahotanni suna tafiya cikin gaskiya, adalci, da inganci.
Stallion Times Da NUJ Sun Horar Da ’Yan Jaridu Kan Yadda Za Su Yi Amfani Da Fasahar AI
Isiyaku Ahmed, Babban Editan Stallion Times, ya jaddada cewa AI na iya sauƙaƙa tattara bayanai da fassara su cikin sauri, amma bai kamata ta maye gurbin ƙa’idodin aikin jarida ba.
“Fasahar AI tana ba da damar tattara bayanai da rarraba su cikin sauri. Amma aikin jarida yana kan ginshiƙan gaskiya, daidaito da adalci. AI ya kamata ta taimaka wajen kare waɗannan ƙa’idoji, ba wajen karya su ba,” in ji Ahmed.
Ayuku Pwaspo, Shugabar NUJ ta Jihar Filato, ta yaba wa Stallion Times bisa shirya horon, tana mai cewa wannan taro ya dace da yanayin aikin jarida na zamani, inda fasahar AI ke ƙara tasiri a fannin labarai.
Mahalarta taron sun nuna gamsuwa da abin da suka koya. Jude Dagwam daga Daily Asset ya ce: “Horon zai taimaka min wajen tattara bayanai da fassarar tattaunawa cikin sauƙi a matsayin ɗan jaridar bincike.”
Karen Keyen daga Radio Nigeria ta bayyana cewa horon ya ƙara mata ilimi kan yadda AI ke tabbatar da amincewar jama’a da bin ƙa’idojin aiki. “Haka nan ya koya min yadda zan yi amfani da kayan aikin AI kamar ChatGPT da Turboscribe wajen fassara sauti zuwa rubutu da inganta aikin edita,” in ji ta.
Wannan horo na daga cikin matakan da Stallion Times da NUJ ke ɗauka don inganta ƙwarewar ’yan jarida, domin fuskantar sabon zamani na labarai cikin ƙwarewa da daidaito.
